Kakakin majalisa ya musanta kwatanta IPOB, 'yan Yarbawa da Boko Haram

Kakakin majalisa ya musanta kwatanta IPOB, 'yan Yarbawa da Boko Haram

  • Kakakin majalisar wakilai ta Najeriya ya musanta bayanan da ke cewa ya kwatanta IPOB da Boko Haram
  • A baya an samu rahotanni da aka yada da ke nuni da hakan, amma Gbajabiamila ya musanta batun
  • Mai magana da yawunsa, ya yi karin haske kan lamarin cikin wata sanarwa da Legit.ng ta samu

Abuja - Kakakin majalisar wakilai, Femi Gbajabiamila ya yi watsi da wasu rahotannin da kafafen yada labarai ke yadawa da ke cewa 'yan arewan IPOB da Yarbawa duk daya ne da Boko Haram da ISWAP.

Lanre Lasisi, mai magana da yawun Gbajabiamila, ya yi karin haske a cikin wata sanarwa da aka aike wa Legit.ng a daren Laraba, 15 ga Satumba.

Kakakin majalisa ya musanta kwatanta IPOB, 'yan Yarbawa da Boko Haram
Shugaban Majalisar Wakilai, Femi Gbajabiamila | Hoto: vanguardngr.com
Asali: UGC

Ya bayyana cewa:

Kara karanta wannan

Rundunar sojin saman Najeriya ta fara bincike kan barin wuta da jirgin yaki ya yi kan fararen hula a Yobe

“Babu inda Shugaban Majalisar ya ambaci sunan wata kungiya. Abin da ya fito fili a cikin jawabin Shugaban Majalisar shi ne mayar da hankali kan ayyukan miyagun mutane da masu aikata laifuka, da tasirin su ga kasar.”

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Jaridar The Nation a baya ta ambato Shugaban Majalisar yana cewa 'yan awaren ba su da bambanci da kungiyoyin 'yan Boko Haram da na ISWAP.

Rahoton ya bayyana cewa Gbajabiamila ya bayyana su a matsayin 'yan ta'adda da ke fakewa da fafutukar ballewa domin su tayar da tarzoma a kan 'yan Najeriya da ba su ji ba ba su gani ba kuma su yi wa tattalin arzikin kasa barna.

Da yan IPOB, da yan Oduduwa, duk yan ta'adda ne kamar Boko Haram: Kakakin Majalisa

Kakakin Majalisar wakilan tarayya, Femi Gbajabiamila, ya bayyana cewa abinda masu rajin ballewa daga Najeriya ke yi kwanakin nan ya nuna cewa basu da banbancin da yan ta'addan Boko Haram.

Kara karanta wannan

'Yan ta'adda da 'yan bindiga sun mamaye murabba'in mita 1,129 na gandun dajin Najeriya

Ya bayyana hakan ranar Laraba a jawabin maraba da mambobin majalisar bayan makonni tara suna hutu, rahoton PremiumTimes.

A ranar 15 ga Yuli, yan majalisar sun tafi hutun shekara. Femi Gbajabiamila yace nan da lokaci kadan, wadannan masu son ballewa daga Naeriya zasu kai Najeriya zuwa ga halaka.

Gwamnatin Buhari ta gargadi Yarbawa kan hada kai da kungiyoyin ta'addanci

A wani labarin daban, Fadar Shugaban kasa a ranar Laraba ta gargadi masu tayar da kayar baya 'yan awaren Yarbawa kan kawance da kungiyar ta'addanci mai fafutukar kasar Biyafra ta IPOB, The Nation ta ruwaito.

Ta bayyana tsoron cewa, alakarsu da IPOB ta sanya alamar tambaya a kan ikirarin su masu rajin kare hakkin Yarbawa ne.

Fadar Shugaban kasa ta nemi Majalisar Dinkin Duniya da ta yi watsi da bukatun da masu tayar da kayar bayan na Yarbawa, membobin IPOB a cikin Kasashen waje da sauran masu kunna rikici kasancewarsu masu rashin daidai da kimar kungiyoyin duniya.

Kara karanta wannan

Da dumi-dumi: ‘Yan bindiga sun kai farmaki gidan yari, sun saki fursunoni 240 sannan suka kashe sojoji a Kogi

Asali: Legit.ng

Online view pixel