Bayan hallaka musulmai sama da 20 a Jos, gwamnati ta sanya dokar hana fita

Bayan hallaka musulmai sama da 20 a Jos, gwamnati ta sanya dokar hana fita

  • wamnatin jihar Filato ta yi Allah wadai da kash-kashen da aka yi wa wasu matafiya a jihar
  • Gwamnati ta gaggauta sanya dokar hana fita domin shawo kan lamarin da kwantar da tarzoma
  • A halin yanzu, an umarci kowa ya zauna a gida daga karfe 6 na yammaci zuwa 6 na safiya

Jos, Filato - Biyo bayan kashe kashen da aka yi a Jos ranar Asabar, gwamnatin jihar Filato ta sanya dokar hana fita na sa’o’i 12 a Jos a kullum daga karfe 6 na yamma zuwa 6 na safe.

Wannan na fitowa ne daga gwamnan jihar ta Filato, Dr Simon Bako Lalong a jiya Asabar 14 ga watan Agusta, 2021 jim kadan bayan tabbatar da kashe-kashen.

Wata sanarwa da gwamnan ya fitar, wacce Legit Hausa ta samo ta nuna gwamnati ta tabbatar da faruwar kashe-kashe a garin, hakazalika ta sanya dokar ta baci.

Kara karanta wannan

Karin haske: An cafke mutane 20 cikin wadanda ake zargi da kisan musulmai a Jos

Yanzu-Yanzu: An sanya dokar ta baci a garin Jos biyo bayan kisan gilla
Taswirar jihar Filato | Hoto: thenationonlineng.net
Asali: UGC

Wani yankin sanarwar na cewa:

"Domin kaucewa ci gaba da tabarbarewar lamarin da kuma kare rayuka da dukiyoyin 'yan kasa, na ba da umarnin sanya dokar hana fita a kananan hukumomin Jos ta Arewa, Bassa da Jos ta Kudu da zai fara daga karfe 6 na yamma zuwa 6 na safe daga yau, 14 ga Agusta 2021.
"Dokar hana fita za ta ci gaba da kasancewa inda kwamitin tsaro na Jiha zai sake dubawa.
"Don haka ana umartar dukkan mazauna da su bi umarnin don ba jami'an tsaro damar kiyaye doka da oda a yankunan da abin ya shafa da kuma magance wadanda ke kokarin haifar da matsala ta hanyar amfani da yanayin don aikata laifi.
"Gwamnati za ta ci gaba da sa ido kan halin da ake ciki tare da daukar karin matakan da suka dace don tabbatar da tsaron rayuka da kadarori."

Kara karanta wannan

Gwamna Masari ya yi barazanar maaka hukumar Kwastam a kotu kan kashe-kashe a Katsina

Gwamna ya jajantawa iyalan wadanda suka mutu

Hakazalika, gwamnan jihar ya mika ta'aziyya ga iyalan wadanda suka mutu, tare da jajantawa wadanda suka ji raunuka.

A cewarsa:

"A yayin da nake ta'aziyya ga iyalan wadanda suka rasa 'yan uwansu, da wadanda suka jikkata a lamarin da bai yi dadi ba, ina kira da a kwantar da hankali tare da yin kira ga 'yan jiharmu da su guji duk wani mataki ko maganganun da za su kara rura wutar lamarin.
"Wannan zunzurtun ta'addanci ne kuma bai kamata a ta'allaka shi da kabila ko na addini ba.
"Mu ci gaba da yin taka tsantsan da sanin ya kamata game da tsaro tare da yin duk mai yuwuwa don wanzar da zaman lafiya da tsaron jihar.

Sojoji sun cafke mutane 12 cikin wadanda ake zargi da kisan musulmai a Jos

A wani labarin, Rundunar tsaro ta musamman, Operation Safe Haven (OPSH) a jihar Filato, ta cafke wasu mutane 12 da ake zargi da aikata kashe-kashe da safiyar Asabar a kan hanyar Rukuba ta karamar hukumar Jos ta Arewa a jihar, in ji rahoton PM News.

Kara karanta wannan

Da gwamnati ta biya kudin fansata, ana sako ni zan yi murabus, Kwamishinan Niger

OPSH ne ke da alhakin wanzar da zaman lafiya a fadin jihar Filato da kewaye.

Manjo Ishaku Takwa, jami’in yada labarai na rundunar, ya bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa ranar Asabar a garin Jos.

Asali: Legit.ng

Online view pixel