Cikakken Bayani: Gwamnan New York Ya Yi Murabus Kan Zargin Cin Zarafin Mata

Cikakken Bayani: Gwamnan New York Ya Yi Murabus Kan Zargin Cin Zarafin Mata

  • Gwamnan New York ta kasar Amurka, Andrew Cuomo, ya yi murabus daga kan mukaminsa
  • Wannan ya biyo bayan matsin lamba da yake sha kan zargin cin zarafin mata da ake masa
  • Cuomo ya musanta zargin inda yace bai aikata ba kuma bai ma taɓa tunanin aikata makamancin haka ba

New York - Gwamna Andrew Cuomo na jihar New York ta kasar Amurka, ya yi murabus daga mukaminsa bisa zargin da ake masa na neman mata, kamar yadda dailytrust ta ruwaito.

Gwamnan ya sha matsin lamba daga mutane da dama na ya sauka da matsayin gwamna bayan wasu mata da dama sun zarge shi da cin zarafinsu.

Ya sanar da matakin murabus ɗinsa ne biyo bayan wani rahoto da ofishin Antoni Janar na jihar ya nuna zarginsa da cin zarafin mata a lokuta da dama.

Gwamnan New York, Andrew Cuomo
Labari da Dumi-Dumi: Gwamnan New York Ya Yi Murabus Daga Kujerarsa Hoto: bbc.com/hausa
Asali: UGC

Gwamna Cuomo ya faɗa ranar Talata cewa:

"Duba da halin da ake ciki, Matakin da ya fi dacewa na dauka wanda zan taimaka shi ne na sauka na bar gwamnati ta cigaba da aikinta,

Kara karanta wannan

Yanzu-yanzu: Ba za'a tsige Uche Secondus daga jagorancin PDP ba, Tambuwal

"Saboda haka na sauka daga matsayin gwamna saboda ku nake wa aiki, kuma aiki mai kyau shine in kyautata muku."

Gwamnan ya alaƙanta lamarin da COVID19

A cikin jawabinsa gwamnan ya yi tsokaci kan halin da ake ciki na korona ga kuma zargin da ake masa, yace:

"Muna cikin wani yanayi na rayuwa ko mutuwa. Ga ayyukan gwamnati kuma ga wasu abubuwa na shagala, wannan shine kololuwar abinda ya kamata gwamnati ta yi. Kuma banason zama sanadin gazawar gwamnati."
"Ina kaunar New York kuma ina kaunar mutanen New York, wannan soyayyar da nake wa jihar mu ita ke karamun karfin guiwa a kan duk abinda na yi. Saboda haka bana son in zama mutum mai son kansa."

Shin ya amsa zargin da ake masa?

Da yake jawabi na musamman ga 'yayansa mata guda uku, Cuomo yace:

"Inason ku sani daga ƙarƙashin zuciyata cewa ban aikata abinda ake zargina da shi ba kuma bantaba tunanin cin zarafin wata mace ba.

Kara karanta wannan

Karin Bayani: WAEC Ta Sanar da Sabuwar Ranar da Za'a Fara Rubuta Jarabawar WASSCE 2021

"Ina girmama kowace mace daidai yadda nikeson naga kowa na girmama su, kuma wannan shine gaskiya guda ɗaya."

Zai sauka daga mulki ne daga nan zuwa kwana 14. Daga nan zai miƙa mulkin ga mataimakiyarsa Kathy Hochul, kamar yadda BBC Hausa ta ruwaito.

A wani labarin kuma An Tafka Ruwan Sama a Rana Daya da Ba'a Taba Irinsa Ba Cikin Shekara 100 a Katsina

A karon farko cikin shekara 100, an tafka wani mamakon ruwan sama a rana ɗaya fiye da yadda aka saba a Kastina.

Shugaban NiMet, Farfesa Mansur Bako Matazu, shine ya bayyana haka a wurin taron kara wa juna sani a Abuja.

Asali: Legit.ng

Online view pixel