An Tafka Ruwan Sama a Rana Daya da Ba'a Taba Irinsa Ba Cikin Shekara 100 a Katsina
- A karon farko cikin shekara 100, an tafka wani mamakon ruwan sama a rana ɗaya fiye da yadda aka saba a Kastina
- Shugaban NiMet, Farfesa Mansur Bako Matazu, shine ya bayyana haka a wurin taron kara wa juna sani a Abuja
- A cewar Matazu, hukumar NiMet reshen Katsina ta gano cewa an zuba ruwan da ya kai milimita 100
Katsina - Yayin da ake fuskantar matsalar ambaliyar ruwa da aka yi hasashen zai shafi wasu sassan Najeriya, hukumar hasashen yanayi (NiMet) tace an tafka mamakon ruwa da yakai kusan milimita 100 a rana ɗaya a Katsina.
Dailytrust ta ruwaito Shugaban hukumar, Farfesa Mansur Bako Matazu, ya bayyana haka a wani taro da NiMet ta shirya a Abuja.
A cewar shugaban NiMet yawan ruwan da aka samu shine kololuwar ruwan da aka taɓa yi a jihar cikin shekara 100, kamar yadda jaridar Linda Ikeji ta ruwaito.
Wane hasashe Hukumar NiMet ta yi?
A jawabin da Matazu yayi wurin taron, yace hukumar ta yi hasashen samun karuwar ruwan sama a tsakanin watan Yuli da Satumba.
Farfesa Matazu yace
“A baya, mun yi harsashen cewa tsakanin watan Yuli da Satumban 2021, za a sami karuwar ruwan sama matuka, wanda zai shafi yankuna da yawa, har ma ya haddasa karamar ambaliya a wasu wuraren.
“A Jihar Katsina alal misali, bincikenmu ya nuna cewa an sami kusan milimita 100 na ruwan sama a rana daya. Ba a taba samun irin haka ba a cikin shekara 100. Hakan na nuna cewa ana samun sauyin yanayi sosai."
Wane dalili ke kawo yawan ruwan sama?
Matazu ya bayyana cewa ana samun karuwar saukar ruwan sama ne daga canjin yanayi.
Sannan ya kara da cewa tsaka-tsakin ruwan sama da aka saba samu a rana ɗaya shine milimita 30.
Matazu ya cigaba da cewa:
"Ana karkasa yanayi ne zuwa gida uku, kuma yanayi na ‘C’ shi ne ake samu a Arewa, wanda shi kuma ya kasu zuwa C1 da C2 da kuma C3. Dalilin da yasa kenan ake tafka ruwa sosai a bana.
A wani labarin kuma sabon rahoton da aka fitar na jerin masu kudin duniya ya nuna cewa Dangote ya koma na 117
Rahoton ya bayyana cewa Aliko Dangote, shugaban kamfanin 'Dangote Group' ya mallaki dukiyar da takai dalar Amurka biliyan $17.8bn.
Wanda yafi kowa kuɗi a duniya a cewar rahoton shine Elon Musk, haifaffen ƙasar Africa ta kudu, wanda ya mallaki dalar Amurka biliyan $194bn.
Asali: Legit.ng