Yanzu-yanzu: Ba za'a tsige Uche Secondus daga jagorancin PDP ba, Shugabannin jam'iyya

Yanzu-yanzu: Ba za'a tsige Uche Secondus daga jagorancin PDP ba, Shugabannin jam'iyya

Jam'iyyar hamayya ta Peoples Democratic Party (PDP) ta ce ba za'a tsige Prince Uche Secondus daga kujerarsa ba amma za'a gaggauta gudanar da taron gangami a Oktoba.

Asali an shirya gudanar da taron gangamin ne a Disamba, karshen shekara.

Gwamna Aminu Waziri Tambuwal na jihar Sokoto kuma shugaban kungiyar gwamnonin PDP ne yayi sanarwar ranar Talata bayan ganawar sirri da masu ruwa da tsaki suka gudanar a Abuja.

A tsokacin da Tambuwal yayi kan barakar dake cikin jam'iyyar, ya ce mambobi sun yarda a hada kai da juna.

Yace:

"Muna farin cikin sanar da cewa mun tattauna dukkan matsaloli kuma mun yanke shawaran cigaba da aiki matsayin 'yan uwa."

Yanzu-yanzu: Ba za'a tsige Uche Secondus daga jagorancin PDP ba, Shugabannin jam'iyya
Yanzu-yanzu: Ba za'a tsige Uche Secondus daga jagorancin PDP ba, Shugabannin jam'iyya
Asali: Original

Asali: Legit.ng

Online view pixel