Yanzu Yanzu: Kotun koli ta yanke hukuncin karshe kan nasarar zaben Akeredolu

Yanzu Yanzu: Kotun koli ta yanke hukuncin karshe kan nasarar zaben Akeredolu

  • Gwamna Rotimi Akeredolu a ranar Laraba, 28 ga watan Yuli, ya sake cin nasara a Kotun Koli da ke Abuja da karamin tazara
  • Wannan ya kasance ne bayan uku daga cikin alkalai bakwai na shari’ar sun yanke hukuncin cewa takarar Akeredolu a zaben gwamnan Ondo bai da tasiri kuma abun sokewa ne
  • Sai dai kuma, tunda sauran alkalan sune suka fi yawa, an tabbatar da nasarar zaben gwamnan na Ondo

Abuja- Kotun Koli a ranar Laraba, 28 ga watan Yuli, ta tabbatar da sake zaben Rotimi Akeredolu a matsayin gwamnan jihar Ondo bayan takaddama mai karfi da Eyitayo Jegede na PDP.

An tabbatar da nasarar Akeredolu bayan alkalai hudu daga cikin bakwai na Kotun Koli da suka saurari karar sun goyi bayan takararsa a zaben na ranar 10 ga Oktoba, 2020 a jihar, Channels TV ta ruwaito.

Yanzu Yanzu: Kotun koli ta yanke hukuncin karshe kan nasarar zaben Akeredolu
Kotun koli ta tabbatar da nasarar zaben Akeredolu Hoto: All Progressives Congress
Asali: Facebook

Sauran alkalan uku ba su yarda da hukuncin mafi rinjaye ba, suna masu jaddada cewa takarar Akeredolu a wancan zaben abun sokewa ne, Leadership ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Ikedi Ohakim: Jam'iyyar APC ta yi babban kamu a jihar Imo

Gwamnan APC ya sake galaba kan ɗan takarar PDP a kotun ɗaukaka ƙara a Ondo

A baya mun kawo cewa, kotun daukaka kara da ke zamanta a Akure, babban birnin jihar Ondo ta yi watsi da karar da dan takarar gwamna a jihar na Peoples Democratic Party, PDP, Mr Eyitayo Jegede ya shigar na kallubalantar nasarar Gwamna Rotimi Akeredolu wanda shine dan takarar jam'iyyar All Progressives Congress, APC a zaben.

The Punch ta ruwaito cewa tunda farko kotun sauraren kararrakin zabe ta yi watsi da karar da dan takarar na PDP ya shigar na kallubalantar zaben saboda rashin kwararran hujojji amma Jegede ya daukaka kara a kotun na gaba.

Premium Times ta ruwaito cewa kotun daukaka karar, bayan ta yi nazari kan dalilai bakwai da mai daukaka karar ya gabatar mata ta yi watsi da karar tana mai cewa ba shi da kwararran hujjoji.

Kara karanta wannan

Darajar Naira ta fadi bayan sanarwan CBN na daina sayarwa yan kasuwar canji Dalar Amurka

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng