Ikedi Ohakim: Jam'iyyar APC ta yi babban kamu a jihar Imo

Ikedi Ohakim: Jam'iyyar APC ta yi babban kamu a jihar Imo

  • Jam’iyyar All Progressives Congress (APC) ta tarbi Ikedi Ohakim, tsohon gwamnan Imo, a cikin inuwarta
  • A cewar Ohakim, ya yanke shawarar ne sakamakon sahihiyar sha'awar da yake da ita na gamsar da bukatun mutanensa da kuma yi musu aiki mai inganci
  • Shugabannin jam’iyyar sun baiwa Ohakim tutar APC a ranar Talata, 27 ga watan Yuli, a karamar hukumar Isiala Mbano na jihar

Isiala Mbano, jihar ImoA karshe tsohon gwamnan jihar Imo, Ikedi Ohakim, ya koma jam'iyyar All Progressives Congress (APC) mai mulki.

A cewar jaridar Vanguard, Ohakim ya koma APC ne a ranar Talata, 27 ga watan Yuli, a mahaifarsa dake Okohia a karamar hukumar Isiala Mbano na jihar inda ya karbi tutar jam’iyyar daga shugaban, Marcellenus Nlemigbo.

Ikedi Ohakim: Jam'iyyar APC ta yi babban kamu a jihar Imo
Ohakim ya ce ya koma APC ne don ra'ayin mutanensa Hoto: Ikedi Ohakim
Asali: Facebook

Tsohon gwamnan ya ce ya yanke shawarar ne domin ra’ayin mutane saboda su ne zabinsa na farko, jaridar The Guardian ta ruwaito.

Kara karanta wannan

An gagara dinke barakar da ta shiga PDP duk da Gwamna ya zauna da Wike, Secondus

Ya bayyana cewa wannan matakin nasa ya yi daidai da abin da mutanensa suke fata don yi musu hidima sosai a kan wani sabon dandamali mai kyau.

Kalaman nasa:

“Imo na ke tunani a kuma zabi ne ci gaba da tafiya kan hanya. Lokacin da dukkanin shuwagabannin APC suka ziyarce ni domin yin rajista a matsayin memban jam’iyyar, sai na fada masu cewa na yanke wannan matsayi ne bisa la’akari da zabin da na yi.
“Ina da wata manufa ta daban da zan shiga siyasa don amfanin kowa ba don son rai ba. A wannan karon na yanke shawarar kada in yi iyo a kan tekun, in da ya kara da cewa "mai masaukin nan su ne za su binne ni lokacin da na mutu kuma tunda ba zan iya binne kaina ba lokacin da na mutu na yanke shawarar yin biyayya ga mutanena."

Ni dai jam'iyyar APC haihata-haihata har abada, Gwamnan Sokoto, Aminu Tambuwal

Kara karanta wannan

Da dumi-dumi: Manyan shugabannin PDP sun sauya sheka zuwa APC, an saki sunayensu

A wani labarin, gwamnan jihar Sokoto, Aminu Waziri Tambuwal, ya bayyana rashin gamsuwarsa da mulkin jam'iyyar All Progressives Congress (APC) inda yace Allah ya kiyaye ya koma APC.

Gwamnan ya caccaki gwamnatin tarayya kan yadda take mulkan yan Najeriya kuma ta jefa yan kasa cikin kunci da talauci.

Tambuwal wanda shine shugaban kungiyar gwamnonin PDP ya bayyana hakan ne yayin taron da gwamnonin jam'iyyar adawa suka yi a jihar Bauchi, rahoton Tribune.

Asali: Legit.ng

Online view pixel