Darajar Naira ta fadi bayan sanarwan CBN na daina sayarwa yan kasuwar canji Dalar Amurka
- Dakatar da sayar da Dala ga yan kasuwar Canji da Bankin kasa ta CBN tayi ta bar baya da kura
- Farashin Naira na cigaba da fadi bisa dala a kasuwar Canji
- CBN ta bayyana dalilin da da yasa ta dau wannan mataki
Lagos - Jim kadan sanarwan da gwamnan bankin CBN, Godwin Emefiele yayi na dakatar da sayar da Dala ga yan kasuwar canji, farashin Dalar ta tashi a kasuwar bayan fagge da na banki.
Alkaluman da aka gani a abokiFX.com, wata shafin da ke tattara farashin kudi a kasuwar bayan faggen Legas, sun nuna cewa a jiya farashin Dala ya tashi daga N504 da aka sayar ranar Litinin zuwa N505.00.
Hakazalika, farashin Naira ta fadi a kasuwar bankuna ranar Talata kamar yadda alkaluman da aka daura kan FMDQ suka nuna, kamar da Premium Times ta ruwaito.
A cewar Alkaluman, an tashi kasuwa jiya a N411.67/$1 sabanin N411.50/$1 da aka tashi ranar Litinin.
Banbancin dake tsakanin farashin a kasuwar banki da na bayan faggen a yanzu ya kai N93.33 a ranar Talata.
Shin me yasa CBN ta dakatar da sayarwa yan kasuwar Canji Dala?
Babbar bankin Najeriya CBN ya haramta sayar da Dalar Amurka ga yan kasuwan canji (BDC).
Gwamnan bankin, Godwin Emefiele, ne ya sanar da hakan a jawabin da ya yiwa manema labarai bayan zaman kwamitin kudi MPC na bankin, rahoton DailyTrust.
Ya ce N5. 7 billion da ake baiwa yan kasuwar canji ba zai yiwu a iya cigaba ba saboda kimanin yan kasuwan canji 5500 ake baiwa $110million kowani mako.
Asali: Legit.ng