Yan bindiga sun saki dan majalisa da abokansa bayan biyan kudin fansan N15m da katin waya na N100,000

Yan bindiga sun saki dan majalisa da abokansa bayan biyan kudin fansan N15m da katin waya na N100,000

Wani tsohon dan majalisan jihar Kogi, Friday Makama Sani, da abokansa shida sun shaki kamshin yanci bayan garkuwa da su da wasu yan bindiga sukayi a Abuja.

Friday Makama tare da abokan nasa sun kubuta ne bayan biyan yan bindigan kudin fansa.

Jaridar Tribune ta ruwaito cewa sai da aka biya yan bindigan kudi milyan 15 da katin waya na N100,000.

Yan bindigan da farko sun bukaci a basu N20 million.

Majiyoyi daga iyalan wadanda aka sace sun tabbatar da cewa an sakesu ranar Asabar.

Yan bindiga sun saki dan majalisa da abokansa
Yan bindiga sun saki dan majalisa da abokansa bayan biyan kudin fansan N15m da katin waya na N100,000
Asali: Twitter

Yan bindiga sun fasa Otal a Abuja

Wasu yan bindiga sun kai farmaki gidan Otal na Hilltop dake garin Tunga Maje a birnin tarayya Abuja da daren Laraba, 24 ga Yuni, 2021.

Daily Trust ta rahoto cewa sun yi awon gaba da mamallakin Otal din, tsohon dan majalisa tare da wasu mutane.

An ce mamallakin Otal din mai sune Prince Adejo, tare da wasu mutane shida na ganawa a ciki lokacin da yan bindigan suka kai farmaki.

Garin Tunan-Maje ta kwan biyu tana fuskantar barazanar yan bindiga.

A cewar mazauna garin, wannan shine karo na biyar da aka kai hari don garkuwa da mutane a shekarar nan.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdul Rahman Rashid avatar

Abdul Rahman Rashid Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin hudu yanzu tare da shararriyar jarida Legit. Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss. Zaku tuntubarta a akwatin email: abdulrahman.rashidah@corp.legit.ng