Instagram ta share shafin Adamu Garba, kwanaki bayan Google ya cire manhajarsa ta Crowwe

Instagram ta share shafin Adamu Garba, kwanaki bayan Google ya cire manhajarsa ta Crowwe

  • Da farko Google ya cire manhajarsa mai suna Crowwe da ake hirarraki da hada-hadar kasuwanci daga Playstore
  • Ya zargi manhajar Twittter da zama tamkar abokiyar gaban da ke neman ruguza Najeriya
  • Ya wallafa sakonnin goyon bayan matakin Shugaba Buhari na dakatar da ayyukan Twitter

Instagram ta goge shafin tsohon dan takarar Shugaban Kasa, Adamu Garba.

Babban Jami’in Rukunin Kamfanin IPI shi ne ya bayyana hakan a shafinsa na Facebook, ranar Laraba.

“Sun goge mini shafina a Instagram kuma. Wannan na iya faruwa kan kowa idan ya yi tsokacin da ya sha bamban da nasu. Wadannan sune dalilan da suka sa lallai mu kara himma kan manhajar Crowwe,” ya rubuta.

Bincike ya nuna cewa tabbas an cire shafin nasa a Instagram din.

Binciken neman sunansa a manhajar, na @adamugarbaii, ya nuna shafin ya zama fayau da wani dan karamin rubutu cewa “ba a samu mai wannan sunan ba.”

Babu karin haske kan ainihin dalilin da manhajar ta Instagram da kamfanin Facebok ya mallaka ya saka shi goge shafin nasa.

Instagram ta share shafin Adamu Garba, kwanaki bayan Google ya cire manhajarsa ta Crowwe
Instagram ta share shafin Adamu Garba, kwanaki bayan Google ya cire manhajarsa ta Crowwe
Asali: Instagram

Sai dai lamarin na zuwa ne a ganiyar sukar da ake masa kan goyon bayan Shugaba Muhammadu Buhari kan matakin da ya dauka na dakatar da manhajar Twitter a Najeriya.

Sannan hakan na kuma faruwa ne kwanaki bayan shafin Google ya cire manhajar Crowwe, wacce ake amfani da ita wajen aika wa tare da karbar sakonnin hira da hada-hadar kudi daga kan shafin Google din na Playstore.

A baya dai tsohon dan takarar Shugaban Kasar ya zargi Twitter da zama ‘wata kafar da ke yaki da Najeriya’, yana mai cewa manhajar na kokarin ganin kasar Najeriya ta wargaje cikin shekara biyun da suka gabata.

Yace:

“Eh, ina jin dadi, kwarai da gaske. Hakan ya nuna duk abin da mutum ya aikata zai girbe aikinsa,”.
“Idan har kun karanci take-taken Twitter a cikin shekara biyun da suka gabata, za ku ga cewa kafar ta zama wani dandali mai yaki da wanzuwar Najeriya.
‘’Babu abin da take yi illa neman wargaza kasar maimakon ta zama kafar fadar albarkacin baki.”

Asali: Legit.ng

Online view pixel