Bayan yan makonni 3 da Sulhu, Isra'ila ta sake kaiwa Falasdinawa hari
• Jirgin yaki ya kaddamar da sababbin hare-hare a kan yankunan da mayakan Hamas ke zaune a Zirin Gaza
• Sojoji sun ce martani ne ga ababen fashewa da Hamas ta harba zuwa Kudancin Isra’ila
• Isra’ila ta ce tana cikin shirin duk wani martanin da za a mayar ko da sabon yaki ne
Jiragen yakin sojin Isra’ila sun kaddamar da sababbin hare-hare kan kungiyar Hamas a Zirin Gaza, wanda hakan ya kawo karshen takaitaccen tsagaita wutar da aka cimma bayan mummunan fadan da ya barke a yankin a baya bayan nan.
Wata sanarwa da rundunar tsaron Isra'ila IDF ta fitar, ta ce jiragen yakinta sun kai hare-hare kan wasu gine-gine na rundunar da ke kare yankin Khan Yunis a cikin birnin Gaza, rahoton Daily Mail.
Ta kuma ce ayyukan ta'addanci na aukuwa a wadannan wuraren, kuma rundunar a shirye take ta tunkari dukkan martanin da zai biyo baya, wadanda suka hada da ci gaba da kai hari a Zirin Gaza.
Sojojin Isra'ilar sun harba rokokin kan Gazan a mastayin ramuwar gayya, bayan tashin gobara a yankunanta da dama sakamakon ababen fashewa da kungiyar Hamas ta harba.

Asali: UGC
A karon farko tun bayan kawo karshen rikicin kwanaki 11 a zirin Gaza, wanda ya yi sanadiyar mutuwar Falasdinawa sama da 200, Isra'ila ta kaddamar da hare-haren ramuwar gayya zuwa zirin gaza, bayan da kungiyar Hamas ta harba balam-balam masu fashewa da suka haddasa gobara a wasu yankunan Isra'ilar.
Matakin ya biyo bayan wani maci da Yahudawa masu tsanannin kishin kasa suka yi a yankin gabashin birnin Qudus a ranar Talatar nan, wanda ya haifar da kakkausar suka daga kungiyar Hamas,da ita ce kungiyar da ke iko da yankin na Gaza a hukumance, riwayar France24.
Sai dai ba a tabbatar ko akwai wadanda wannan harin ya jikkata ba.
Falasadinawa sun lashi takobin kwato Kudus
Wani kakakin Hamas ya fitar da wata sanarwa a Twitter yana cewa Falasdinawa za su ci gaba da "jajircewar da suke yi da kare 'yancinsu da yankuna masu tsarki" a birnin Qudus.
Hukumar kashe gobara ta Isra'ila ta ce balan-balan din da mayakan Hamas suka harba sun haifar da gobara kimanin 20 a wasu yankunan Kudancin Isra'ila.
Asali: Legit.ng