Babban Hadimin Gwamna ya ki bin sa zuwa APC bayan ya bar PDP, ya zabi ajiye masa aikinsa
- Mark Obi ya ajiye kujerarsa na Mai ba Gwamna Ben Ayade shawara
- Obi ya ce dole ya yi murabus tun da Gwamna ya koma jam’iyyar APC
- Hadimin Gwamnan ya ce yana tare da PDP, ba zai iya sauya-sheka ba
Daya daga cikin masu ba gwamnan jihar Kuros Riba, Dr. Ben Ayade shawara, Mark Obi, ya rubuta takardar murabus, ya ajiye aikinsa.
Jaridar Premium Times ta fitar da rahoto cewa Mark Obi ya sauka daga kujerar da yake kai na mai ba gwamna shawara ne a ranar Litinin.
Mista Mark Obi shi ne mai taimakawa Ben Ayade a kan abubuwan da su ka shafi harkar SDG.
KU KARANTA: Gwamnan K/Riba, Ben Ayade, ya fita daga PDP
Obi ya na cikin wadanda suka kafa jam’iyyar PDP a Kuros Riba, saboda tsananin biyayya ya zabi ya rasa matsayinsa na hadimin gwamna.
A wasikar da ya rubuta, tsohon hadimin ya bayyana cewa a matsayinsa na daya daga cikin kusoshin PDP, ba zai sauya-sheka zuwa APC ba.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
“Bayan abubuwan da suka faru game da alkiblar siyasar gwamnan jiha, dole in sake duba yadda dangantaka ta ke da gwamnatin nan mai-ci.”
“Da hankali na, ba zan iya cigaba da rike mukamin mai bada shawara na musamman a kan manufofin SDG ba.” Inji Obi a wasikar barin aikin.
KU KARANTA: Ayade ya hadu da Buhari bayan ya sauya-sheka
“A dalilin haka, ina mai gabatar da murabus dina ba tare da bata lokaci ba. Ina godiya ga gwamna Ayade da ya bani damar rike wannan matsayi.”
Mista Obi ya ce: “Duk da haka, zan cigaba da ba gwamnati da jihar Kuros Riba duk gudumuwar da zan iya a matsayi na babba kuma mai-ta-cewa.”
Jaridar Vanguard ta ce tsohon mukarrabin ya wakilaci mazabar Boki a majalisar dokokin jiha na shekaru takwas tsakanin shekarar 1999 da 2007.
Dazu kun ji cewa kungiyar BSO ta yi zanga-zanga a Abuja, ta ce kiri-kiri kusoshin Gwamnatin jihar Kano suka hana ayi wa wasu rajista a jihar Kano.
Shugaban kungiyar BSO na Kano, Shehu Dalhatu, ya ce kiri-kiri wasu kusoshin Gwamnatin Kano suka hana ayi wa wasu 'yan APC na asali rajista.
Asali: Legit.ng