Karin Bayani: Gwamnan Cross Rivers Ya Gana da Buhari a Karon Farko Bayan Komawarsa APC

Karin Bayani: Gwamnan Cross Rivers Ya Gana da Buhari a Karon Farko Bayan Komawarsa APC

- Gwamnan Cross Rivers, Ben Ayade, ya ziyarci shugaban ƙasa Buhari a karon farko tun bayan sauya sheƙarsa daga PDP zuwa APC

- Gwamnan ya bayyana ficewara daga tsohuwar jam'iyyar tasa PDP ne a watan Mayu bayan ya gana da wasu gwamnonin APC

- An zaɓi Ben Ayade a matsayin gwamnan Cross Rivers a shekarar 2015, ya kuma sake zarcewa a zaɓen 2019

Shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, ya karɓi bakuncin gwamnan Cross Rivers, Ben Ayade, ranar Alhamis a fadarsa dake Abuja, kamar yadda vanguard ta ruwaito.

KARANTA ANAN: Babbar Magana: PDP Ta Buƙaci Wani Gwamna Yayi Murabus Daga Muƙaminsa

Farfesa Ben Ayade, a kwanan nan ne ya fice daga jam'iyyar PDP ya koma jam'iyya mai mulki ta APC.

Wannan ziyara da yakaiwa shugaba Buhari tazo dai-dai mako biyu da sauya shekarsa daga PDP.

Da Ɗumi-Ɗumi: Shugaba Buhari Ya Gana da Gwamnan Cross Rivers, Ben Ayade, Bayan Komawarsa APC
Da Ɗumi-Ɗumi: Shugaba Buhari Ya Gana da Gwamnan Cross Rivers, Ben Ayade, Bayan Komawarsa APC Hoto: @BashirAhmad
Asali: Twitter

Gwamnoni shida na APC ne suka tarbi, Gwamna Ayade, cikinsu harda shugaban kwamitin riko na jam'iyyar APC, Mai Mala Buni, tare da wasu yan majalisun tarayya, kamar yadda channels tv ta ruwaito

Gwamna Ayade yace kafin komawarsa APC, ya kasance mamba da ya sadaukar da kansa ga tsohuwar jam'iyyarsa PDP.

KARANTA ANAN: Najeriya Zata Samar Da Manyan Wayoyin Hannu Ga Ƙasashen Africa, Pantami

Yace har yanzun yana girmama PDP, saboda itace jam'iyyar da ta bashi tikitin takara kuma ta mara mishi baya yaci zaɓen sanata dana gwamna a jere.

Legit.ng hausa ta gano cewa, An zaɓi Ayade a matsayin gwamnan Cross Rivers a shekarar 2015 ƙarƙashin inuwar jam'iyyar PDP, ya kuma sake ɗarewa kan kujerarsa a karo na biyu a zaɓen 2019 duk ƙarƙashin PDP.

Amma a watan Mayu da ya gabata, gwamna Ayadeya bayyana ficewarsa daga PDP zuwa jam'iyyar APC

A wani labarin kuma Babbar Magana: PDP Ta Buƙaci Wani Gwamna Yayi Murabus Daga Muƙaminsa

Jam'iyyar hamayya ta PDP reshen jihar Imo tayi kira ga gwamnan jihar yayi murabus daga kujerarsa.

PDP tace gwamnan bashi da karsashi ko ƙwarin guiwar da zai fuskanci matsalar tsaron da take kara yawaita a jihar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel