Yanzu-yanzu: Gwamnan Kross Ribas, Ben Ayade, ya fita daga PDP, ya koma APC

Yanzu-yanzu: Gwamnan Kross Ribas, Ben Ayade, ya fita daga PDP, ya koma APC

- Jam'iyyar PDP ta yi babban rashi na siyasa a ranar Alhamis

- Wannan ya tilastawa uwar jam'iyyar shiga ganawar gaggawa a Abuja

- Gwamnonin APC akalla 6 suka dira Kross Riba don tarban gwamnan

Labarin da ke shigo mana da duminsa na nuna cewa gwamnan jihar Kross Ribas, Ben ayade, ya sauya sheka daga jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) zuwa jam'iyyar All Progressives Congress (APC).

Gwamna Ayade ya sanar da hakan ne da safiyar Alhamis a ganawar da yayi da gwamnonin APC shida da suka kai masa ziyara gidan gwamnatin jihar, riwayar ChannelsTV.

Legit ta tattaro cewa gwamnonin sun hada da gwamnan Kebbi, Atiku Bagudu; gwamnan Yobe, Mai Mala Buni; gwamnan Plateau, Simon Lalong; gwamnan Jigawa, Badaru Talamiz; da gwamnan Ekiti, Kayode Fayemi.

DUBA NAN: El-Rufai: Ƙarɓar Haraji Daga Yan Najeriya Ne Zai Iya Farfado da Tattalin Arziki Ba Kudin Man Fetur Ba

Yanzu-yanzu: Gwamnan Kross Ribas, Ben Ayade, ya fita daga PDP, ya koma APC
Yanzu-yanzu: Gwamnan Kross Ribas, Ben Ayade, ya fita daga PDP, ya koma APC
Asali: Original

KU KARANTA: Gwamna El-Rufai ya yi wa Gwamnoni kaca-kaca, NGF ta bukaci a koma saida litar fetur N408

A ranar Laraba, gwamnonin Najeriya 36 sun hadu domin tattauna lamarin cire tallafin man fetur.

A kwanakin baya, kungiyar gwamnonin Najeriya NGF karkashin Gwamna Kayode Fayemi, ta kafa kwamiti na musamman domin duba lamarin cire tallafin man fetur.

Gwamnonin sun yi bayanin cewa ba zai yiwu a cigaba da biyan kudin tallafin mai ba saboda masu fashin kwabri da manyan yan kasuwa kawai ke amfana.

Saboda haka sun bada shawaran cewa a cire tallafin mai domin ceton tattalin arzikin Najeriya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdul Rahman Rashid avatar

Abdul Rahman Rashid Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin hudu yanzu tare da shararriyar jarida Legit. Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss. Zaku tuntubarta a akwatin email: abdulrahman.rashidah@corp.legit.ng