Kungiyar Farar Hula Ta Soki Shugaban ’Yan Sanda Kan Kalaman Hada Jami’ansa da NSCDC

Kungiyar Farar Hula Ta Soki Shugaban ’Yan Sanda Kan Kalaman Hada Jami’ansa da NSCDC

  • Kungiyar farar hula ta yi martani mai zafi ga sufetan 'yan sanda bisa kalamansa na neman a hada hukumar tsaro ta NSCDC da 'yan sanda
  • Shugaban kungiyar, Rabaran Solomon Semaka ne ya yi martanin yana mai cewa hukumar 'yan sanda ne ke bukatar gyara a halin yanzu
  • Ya kuma kara da lissafo wasu matakai na musamman da gwamnatin Najeriya ya kamata ta dauka domin kara cigaban hukumar NSCDC

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Wata kungiyar farar hula mai rajin kare hakkin 'yan Najeriya ta caccaki kalaman sufeton 'yan sanda a kan haɗa jami'an tsaron NSCDC da jami'an hukumar kiyaye hadura ta kasa FRSC wuri ɗaya da 'yan sanda.

Kara karanta wannan

Lauyoyi sun yi zanga zangar rashin yadda da kama Yahaya Bello a kotun koli

In ba a manta ba dai shugaban 'yan sanda ya yi kira ne a kan ya kamata a hada jami'an tsaron guda biyu da 'yan sanda wanda a cewarsa ba su da wani bambanci.

Police IG
Kungiyar farar hula ta ce hada 'yan sanda da NCDC zai ruruta matsalar staro. Hoto: Nigerian Police Force
Asali: Facebook

Hada jami'an 'yan sanda da NSCDC

Jaridar Leadership ta ruwaito shugaban kungiyar farar hular, Rabaran Solomon Semaka, yana Allah wadai da kalaman hukumar ta 'yan sanda yana mai cewa hukumar 'yan sanda ne ke bukatar kwaskwarima.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Rabaran Semaka ya kara da cewa abun mamaki ne matuka ace za a hada jami'an tsaron NSCDC da 'yan sanda kuma hakan zai kawo tasgaro ga tsaron kasar baki daya.

Saboda haka ya ce ya zama wajibi su fito su nuna rashin amincewarsu da wannan kuduri na shugaban 'yan sandan.

A cewarsa ayyuka sun riga sun yi wa 'yan sanda yawa saboda haka bai kamata su fito suna neman karin aiki ba.

Kara karanta wannan

NDLEA ta gargadi matafiya kan hanyar da ake iya aukawa cikin matsala

Kokarin hukumar NSCDC

Shugaban kungiyar har ila yau ya lissafo bajinta da jami'an tsaron NSCDC su ka yi a baya wanda ya nuna suna aiki tukuru, cewar jaridar Blueprint

A cewarsa a cikin makonni kadan da suka wuce ne jami'an NCDS suka lalata wasu matatun mai guda 10 waɗanda aka ginasu ba bisa ka'ida ba.

Ya kuma kara da cewa rundunar ta NSCDC ta nuna bajinta a kan yaki da hakar ma'adinai ba bisa ka'ida ba a fadin ƙasar.

Rabaren din ya tabbatar da cewa a bisa wannan namijin kokari da jami'an NSCDC ke yi, dukkan 'yan Najeriya suna yaba musu da kuma goyon bayan su.

Kira kan inganta hukumar NSCDC

A karshe Rabaran Semaka ya yi kira ga gwamnati da ta kara ba wa hukumar tsaro ta NSCDC kulawa ta musamman saboda gudumawa da suke bayarwa.

Ya ce akwai bukatar kara wa jami'an kudin albashi tare da goyon bayan dukkan tsare-tsarensu da kuma sa kafar wando da duk wanda zai kawo musu cikas.

Kara karanta wannan

Kwara: Gwamnati ta fara bincike kan zargin ana sayar da naman shanu mai guba

Yan sanda sun kama tabar wiwi a Legas

A wani rahoton kuma, kun ji cewa rundunar 'yan sandan jihar Lagos ta sanar da kama wani mutum dauke da buhun tabar wiwi guda 30 a yankin Ojo

A cewar mai magana da yawun rundunar, Benjamin Hundeyin sun kama mutumin ne ranar Laraba da asuba

Asali: Legit.ng

Online view pixel