Yanzu-Yanzu: 'Yan Sanda Sun Harbi Tsohon Dan Takarar Shugaban Kasa, Sowore a Abuja

Yanzu-Yanzu: 'Yan Sanda Sun Harbi Tsohon Dan Takarar Shugaban Kasa, Sowore a Abuja

'Yan sanda a babban birnin Tarayya Abuja sun harbi mawallafin jaridar Sahara Reporters kuma tsohon dan takarar shugaban kasa yayin wata zanga-zanga a bakin Unity Fountain dake a Abuja.

An harbiu Sowore a gefen dama a cinya lamarin da ya sa aka yi gaggawan wucewa dashi asibiti.

Da Dumi- Dumi: 'Yan Sanda Sun Harbe Sowore Yayin Zanga-Zanga a Abuja
Da Dumi- Dumi: 'Yan Sanda Sun Harbe Sowore Yayin Zanga-Zanga a Abuja Hoto: thegeniusmedia.com.ng
Asali: UGC

Ya rubuta a shafin Tuwita:

"Yanzun nan 'yar sanda, ACP Atine ta harbe ni a Unity Fountain a Abuja. #RevolutionNow Yanzu aka fara gwagwarmaya za ta ci gaba koda kuwa za su dauki raina!"

Kalli bidiyon lokacin da abin ya faru.

Karin bayani nan kusa...

Asali: Legit.ng

Online view pixel