Matasa sun banka wuta kofar fadar Sarkin Zurmi a jihar Zamfara

Matasa sun banka wuta kofar fadar Sarkin Zurmi a jihar Zamfara

- Wasu mazauna garin Zurmi sun nuna bacin ransa kan hare-haren da yan bindiga ke kai musu

- Fusatattun matasan sun huce fushinsu kan Sarkin Zurmi

- Jihar Zamfara na cikin jihohin da ke fuskantar matsalar tsaro a Arewacin Najeriya

Fusatattun matasa sunyi zanga-zanga kan irinsu kisan awakin da yan bindiga ke musu a karamar hukumar Zurmi ta jihar Zamfara.

Wannan fushi ya kaisu ga banka wuta fadar Sarkin Zurmi.

Bidiyon da TVCNews ta samu ya nuna yana wasu matasa ke kona wasu sashen fadar.

Kawo yanzu, hukumar yan sanda da gwamnatin jihar basu magana kan lamarin ba.

KU KARANTA: Nan da watan Yuli zamu fara ginin layin dogon Kaduna zuwa Kano, Minista Amaechi

DUBA NAN: Daliban jami'ar Kimiyya ta Wudil sun yi bikin murnar ranar Abaya

A bangare guda, gwamnatin jihar Zamfara ta ce tubabbun yan bindigan da suka addabi jihar a baya kawo yanzu sun ajiye makamai sama da dubu guda karkashin shirin sulhun da gwamnatin ta yi.

Kwamishanan tsaro da harkokin cikin gidan jihar, Garba Dauran, ya bayyana hakan ga manema labarai a Gusau, birnin jihar.

Dauran ya ce an lissafa jerin kananan da manyan makamai da albursai da yan bindigan suka ajiye.

Matasa sun banka wuta kofar fadar Sarkin Zurmi a jihar Zamfara
Matasa sun banka wuta kofar fadar Sarkin Zurmi a jihar Zamfara Hoto: Presidency
Asali: Twitter

Asali: Legit.ng

Online view pixel