Daga yanzu, an hana Sallah da na'urar amsa kuwa a Saudiyya illa kira da Iqamah

Daga yanzu, an hana Sallah da na'urar amsa kuwa a Saudiyya illa kira da Iqamah

Ma'aikatar harkokin addinin Musulunci na kasar Saudiyya a ranar Lahadi ta bayar da sabbin umurni game da amfani da na'urar amsa kuwa watau Sifika na waje a masallatai.

A sabon umurnin da ma'aikatar ta bada, daga yanzu kira Sallah da Iqamah kadai za'a iya amfani da Sifikun waje.

Wannan sabuwar doka ta game dukkan Masallatan Khamsu-Salawaati na masarautar amma an togaciye Masallatan Juma'ah da Masallacin Makkah da Madina, rahoton Haramain Sharifain.

A baya, ana Sallolin farilla biyar da wasu Salloli da Sifiku a bayyane a Masallatan Saudiyya.

Amma daga yanzu, za'a yi kiran Sallah da Sifikun waje sannan a yi ainihin Sallah da sifikun cikin Masallatai kadai.

Daga yanzu, an hana Sallah da na'urar amsa kuwa a Saudiyya illa kira da Iqamah
Daga yanzu, an hana Sallah da na'urar amsa kuwa a Saudiyya illa kira da Iqamah

A riwayar BBC, an nakalto kalaman ministan harakokin addini na ƙasar Abdul Latif Al Sheikh na cewa duk wanda ya saɓa wannan sabon umurni zai fuskanci fushin hukuma.

Ma’aikatar ta ce manyan malamai irinsu Sheikh Salih bin Fawzan al-Fawzan da marigayi Sheikh Muhammad bin Salih al-Uthaymin sun bayar da fatawa da ya karfafa wannan qadiyya.

Duk da haka, wasu Musulmai a fadin duniya na sukan wannan mataki da gwamnatin Saudiyya ta dauka inda wasu suka soki Yarima mai jiran gado, Muhammad bin Salman.

Legit Hausa ta tattauna da wani Malamin addini, Malam Tahir Usman Sokoto, wanda ya yi karatun Digirinsa a jami'ar Islamiyya dake birnin Madina a Saudiyya don jin ta bakinsa kan kan lamari.

A cewar Sheikh Tahir Sokoto, yace a kasar Saudiyya ta banbanta da kasashe irin namu saboda ba ta yanke wani shawara na addini ba tare da sa hannun manyan Malamai ba.

A cewarsa: "A Saudiya ba su yi abu a jahilce, duk abinda ka ga sun fito da shi sai sun dubi mahanga ta addini game da shi kafin su zartar da shi. Ba irin kasarmu ba kawai da mutum zai yi tunanin abu ya aikata. Gwamnatin can ba ta aikata abu sai da Malamai."

"Ba matsala bane gaskiya, saboda ba'a cewa rashin amfani da lasfika a addini ya zama matsala saboda asalin abu za'a duba. Ka ga asalin abu ba da lasfika ake Sallah ba, bai yiwuwa ace don a janye sai ya zama matsala a addini."

Asali: Legit.ng

Online view pixel