Da dumi-dumi: Yan bindiga sun kashe limamin Katolika, sun sace wani a Katsina

Da dumi-dumi: Yan bindiga sun kashe limamin Katolika, sun sace wani a Katsina

- Yan bindiga sun kashe limamin katolika, Rev. Fr. Alphonsus Bello, a cocin St. Vincent Ferrer Catholic Church Malunfashi, jihar Katsina

- Maharan sun kuma yi garkuwa da wani tsohon limamin cocin, Rev. Fr. Joe Keke

- Lamarin ya afku ne a ranar Alhamis, 20 ga watan Mayu

Wasu yan bindiga da ba a san ko su wanene ba sun kashe wani limamin katolika, Rev. Fr. Alphonsus Bello, yayinda suka yi garkuwa da wani, Rev. Fr. Joe Keke a cocin St. Vincent Ferrer Catholic Church Malunfashi, jihar Katsina, jaridar Vanguard ta ruwaito.

An tattaro cewa yan bindigan, a daren ranar Alhamis, sun afkawa cocin Katolika sannan suka fara harbi ba kakkautawa a iska, lamarin da ya jikkata wasu mutane.

KU KARANTA KUMA: Sojojin 'Yan ta'addan ISWAP 300 da aka yi wa horo a Libya suka yi sanadiyyar mutuwar Shekau

Da dumi-dumi: Yan bindiga sun kashe limamin Katolika, sun sace wani a Katsina
Da dumi-dumi: Yan bindiga sun kashe limamin Katolika, sun sace wani a Katsina Hoto: @PremiumTimesng
Asali: UGC

Daraktan sadarwa na Sakatariyar Katolika ta Najeriya, Padre Mike Umoh, wanda ya tabbatar da faruwar lamarin, ya ce wadanda ake zargin sun jefar da gawar Fr Alphonsus Bello a cikin gonar da ke bayan Makarantar Horarwa ta Catechetical, Malunfashi yayin da har yanzu ba a san inda Fr. Joe Keke yake ba.

Ya ce, “A daren jiya, wasu’ yan bindiga da ba a san ko su waye ba sun far wa daya daga cikin cocin Diocese na Sokoto - St. Vincent Ferrer Catholic Church Malunfashi, da ke jihar Katsina.

“An sace wasu limamai biyu, Frs. Joe Keke da Alphonsus Bello. Fr Keke, tsohon limamin Ikklesiya, yana cikin kusan shekaru 70 yayin da Fr. Bello, limamin Ikklesiya na yanzu, bai wuce shekaru 30 ba.

“A safiyar yau (Juma’a) an tsinci gawar Fr Alphonsus Bello babu rai a gonar da ke bayan Makarantar Horarwa ta Catechetical, Malunfashi. Sai dai kuma, har yanzu ba a san inda Fr. Joe Keke yake ba. Ba a tuntube mu ba kawo yanzu.”

Jaridar Daily Post ta ruwaito cewa tuni mutane suka taru a gaban cocin domin nuna alhini kan lamarin.

A halin yanzu, wata majiya mai tushe daga cocin Katolika ta Sakkwato ta ce marigayin ya kasance dan kungiyar Archdiocese na Kaduna, amma yana tare da na Sokoto kuma an tura shi zuwa cocin Malumfashi da ke Katsina.

A gefe guda, manyan shugabannin yan bindigan jihar Zamfara, Dogo Gide da Black 'Baki' sun ja kunnen manoman wasu yankuna akan cewa sai sun fara musu aikin gonakinsu kafin su bar su suyi nasu a wannan daminan.

KU KARANTA KUMA: Isra’ila da Hamas Sun Amince Da Tsagaita Wuta Bayan Kwana 11 Ana Rikici

Domin gujewa abinda zai kai ya kawo, Daily Trust ta gano cewa wasu daga cikin mazauna yankunan sun fara aiki a gonakin shugabannin yan bindigan tun yanzu.

Wani mazaunin garin Dansadau mai suna Bilyaminu Dansadau ya sanar da Daily Trust cewa wasu daga cikin manoman kauyukan dake kusa da Babbar Doka dake kusa da Dansadau a karamar hukumar Maru, sun fara zuwa gonar Dogo Gide domin gyaranta.

Asali: Legit.ng

Online view pixel