Yanzu-yanzu: Yan bindiga sun kai farmaki Abuja, sun hallaka dan sanda, sun kwashe mutum 2

Yanzu-yanzu: Yan bindiga sun kai farmaki Abuja, sun hallaka dan sanda, sun kwashe mutum 2

Wani jami'in dan sanda ya rasa rayuwarsa yayinda yake kokarin hana garkuwa da mutane a unguwar Tungan-Maje dake karamar hukumar Gwagwalada a birnin tarayya Abuja.

Wannan abu ya faru da safiyar Talata, 13 ga watan Afrilu, 2021.

Wani mazaunin unguwar, Ibrahim Saidu, ya bayyana cewa yan bindigan sun dira garin ne inda suka budewa yan sanda da yan banga wuta.

Saidu ya ce yan bindiga sun fara kai hari Anguwar Samu inda suka yi awon gaba da mutum biyu bayan musayar wuta da jami'an tsaro na tsawon awa guda.

"Gaba daya al'ummar anguwar Samu sun cika da fargaba sakamakon harbe-harben da suka ji, amma abin takaicin shine sun samu nasarar sace mutum biyu," yace.

Ya ce an garzaya da jami'in dan sanda da dan bangan da suka jikkata asibiti.

Yanzu-yanzu: Yan bindiga sun kai farmaki Abuja, sun hallaka dan sanda, sun kwashe mutum 2
Yanzu-yanzu: Yan bindiga sun kai farmaki Abuja, sun hallaka dan sanda, sun kwashe mutum 2
Asali: Depositphotos

Kakakin ‘yan sanda na babban birnin tarayya, ASP Mariam Yusuf, wacce ta tabbatar da mutuwar jami’in 'yan sandan a cikin wata sanarwa, ta ce an kama wasu.

"Rundunar 'yan sanda ta kaddamar da wani shiri na kwato mutane hudu da aka sace daga Dankusa wanda har yanzu ke hannun 'yan bindigan wadanda suka tsere zuwa dajin da ke iyaka da babban birnin tarayya da kuma jihar Neja," in ji ta.

Ta ce kwamishinan 'yan sanda na babban birnin tarayya, Bala Ciroma, ya jajantawa dangin wannan jami'in da ya ba da mafi girman tukuici ga kasar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel