Jerin wadanda suka rike mukamin shugaban hukumar EFCC a tarihin Najeriya
Hukumar hana almundahana da yiwa tattalin arzikin kasa zagon kasa watau EFCC na daya daga cikin hukumomin yaki da rashawa biyu dake Najeriya tun komawarta demokridayya a 1999.
Hukumar na da alhakin binciken ha'inci da almundahanan kudi da ma'aikatan gwamnati, hakazalika masu damfarar mutane.
A kwanakin bayan nan, hukumar ta samu nasarori da dama wajen kama yan damfarar yanar gizo wadanda akafi sani da 'yahoo boys'.
Cif Olusegun Obasanjo ne ya kafa hukumar EFCC a shekarar 2003 domin yakan jami'an gwamnatin Najeriyan da suka sace dukiyan al'umma.
Legit ta kawo muku jerin wadanda suka jagoranci wannan hukumar daga 2003 zuwa yanzu:
Nuhu Ribadu (2003 - 2007)
Farida Waziri (2008 - 2011)
Ibrahim Lamorde (2011 - 2015)
Ibrahim Magu (Mukaddashi 2015 -2020)
Mohammed Abba (Mukaddashi 2020 - 2021)
Abdulrasheed Bawa (Mukaddashi 2021 - Kawo yanzu)
KU KARANTA: Jimoh Ibrahim: Attajirin da Gwamnatin Buhari ta karbewa kadarori ya gaza dawo da su ta kotu
DUBA NAN: Yan majalisar wakilan tarayya 2 sun sauya sheka zuwa jam'iyyar APC
Yawancin wadannan mutane da suka rike wannan hukuma basu kammala wa'adinsu ba face an dakatad da su ana zarginshi da wani laifi.
Na karshe-karshe shine Ibrahim Magu wanda gwamnatin shugaba Buhari ta dakatad kan zargin sayarwa abokansa dukiyoyin da hukumar ta kwace daga hannun barayin gwamnati.
Har yanzu, ba'a gurfanar da Ibrahim Magu a kotu don amsa wannan laifi ba.
An bukaci shugaba Muhammadu Buhari da ya gabatar da rahoton kwamitin shari’a kan tsohon Mukaddashin Shugaban Hukumar EFCC, Ibrahim Magu.
A cikin wata wasika da aka aika wa shugaban, babbar kungiyar kawancen yaki da cin hanci da rashawa ta duniya ta nuna matukar damuwar cewa an tsoma bakin siyasa a cikin aikin EFCC.
Ta kuma bayyana gazawar mahukuntan Najeriya wajen fitar da rahoton dake da alhakin faduwar Najeriya a kwanan nan a shirin yaki da cin hanci da rashawa da kungiyar Transparency International ta yi.
Asali: Legit.ng