Jimoh Ibrahim: Attajirin da Gwamnatin Buhari ta karbewa kadarori ya gaza dawo da su ta kotu

Jimoh Ibrahim: Attajirin da Gwamnatin Buhari ta karbewa kadarori ya gaza dawo da su ta kotu

- Alkali ya ba Gwamnati gaskiya a shari’ar da AMCON ta ke yi da Jimoh Ibrahim

- Jimoh Ibrahim ya nemi kotu ta hana hukumar AMCON karbe wasu kadarorinsa

- Kotu ta yi watsi da karar da ‘dan kasuwar da ake bi bashin Biliyan 69.4 ya shigar

Babban ’dan kasuwar nan, kuma tsohon ‘dan takarar gwamnan jihar Ondo, Jimoh Ibrahim, bai iya dawo da kadarorinsa da hukumar AMCON ta karbe ba.

Jimoh Ibrahim ya rasa karar da ya kai gaban kotu, ya na kalubalantar matakin da AMCON mai kula da kadarorin gwamnati ta dauka a kansa a kwanaki.

Fitaccen attajirin ya dumfari babban kotun tarayya da ke Legas ya na neman ayi fatali da damar da aka ba AMCON na karbe wasu kadarorin da ya mallaka.

Da aka zauna a kotu, Daily Trust ta ce Alkali mai shari’a Rilwan Aikawa, ya zartar da hukunci cewa AMCON ta na da hurumin da za ta karbe kadarorin.

KU KARANTA: Jimoh Ibrahim ya sha kashi a kotun koli

Alkalin ya tabbatar da cewa hukumar AMCON ta bi duk ka’idojin da su ka dace kafin ta karbe dukiyar ‘dan kasuwan, don haka ya ki amince wa da rokonsa.

Daga cikin kadarorin Jimoh Ibrahim da aka karbe akwai ginin NICON Investment Ltd da ke kan titin Muhammadu Buhari Way a cikin birnin tarayya, Abuja.

Haka zalika hukumar ta karbe ginin otel dinsa na NICON Hotels Ltd da ke hanyar Port-Harcourt Crescent a kusa da layin Gimbiya, duk a birnin tarayya, Abuja.

Ba a nan kadai AMCON ta tsaya ba, ta karbe wani katafaren ginin NICON Lekki Ltd da ke Legas.

KU KARANTA: Gwamnatin Akwa Ibom ta karyata zargin facaka da Biliyoyi

Jimoh Ibrahim: Attajirin da Gwamnatin Buhari ta karbewa kadarori ya gaza dawo da su ta kotu
Jimoh Ibrahim Hoto: www.nigeriagalleria.com
Asali: UGC

Ibrahim ya yi ikirarin cewa jami’an AMCON ba su tsaya sun yi bincike kafin su shiga karbe kadarorin da ya mallaka ba, amma kotu ba ta ba shi gaskiya ba.

Lauyan ‘dan kasuwar ya nemi AMCON ta biya shi Naira biliyan 50, amma an yi watsi da wannan roko.

A watan Nuwamban shekarar bara ne Hukumar AMCON mai alhakin kula da kadarorin Najeriya, ta ce ta karbe wasu dukiyoyi da wannan attajiri ya mallaka.

An rufe duk wasu asusun banki da ke dauke da sunan Jimoh Ibrahim da kamfanoninsa; Global Fleet Oil & Gas Limited saboda ya gaza biyan bashin banki.

M. Malumfashi ma'aikacin jaridar Legit.ng ne wanda ya shafe kusan shekaru 5 ya na wannan aiki. Ya yi Digirin farko a ilmin komfuta da Digirgir a harkar bayanai, kuma ya na Digirgir a ilmin aikin jarida.

Malumfashi ya kan buga labarai, ya yi rubuce-rubuce a harkar siyasa, wasanni da addini. Ya yi rubuce-rubuce barkatai a gidajen jaridun Najeriya.

A bibiye shi a Twitter @m_malumfashi

Asali: Legit.ng

Online view pixel