Yan majalisar wakilan tarayya 2 sun sauya sheka zuwa jam'iyyar APC
- Jam'iyyar APC ta samu karuwa a majalisar wakilan tarayya
- Wannan karon, babu dan jam'iyyar PDP ko daya cikin wadanda suka sauya shekan
Yan majalisar wakila tarayya biyu, Blessing Onuh (APGA-Benue) da Yakubu Abdullahi (PRP-Bauchi) sun sauya sheka jam'iyyar All Progressives Congress (APC), Premium Times ta ruwaito.
Sanar da sauya shekarsu ranar Talata a zauren majalisar, Mrs Onuh ta ce ta fita daga jam'iyyar APGA ne saboda rikicin shugabancin da jam'iyyar ke fama da shi a jiharta.
Ta ce sai da ta nemi shawarin mutane sosai kafin yanke shawaran fita daga jam'iyyar.
Hakazalika, Yakubu Abdullahi, ya ce ya sauya sheka daga jam'iyyar PRP saboda "rabuwar kai, rikice-rikice, fadace-fadace da rashin jituwa tsakanin yayan jam'iyyar."
Kawo yanzu, mambobin majalisar wakilai bakwai suka sauya sheka zuwa wata jam'iyyar tun lokacin da aka shiga majalisa ta 9 a 2019.
A watan Junairu, Sam Onuigbo, mai wakiltar Ikwuano/Umuahia na jihar Abia ya fita daga PDP zuwa APC.
DUBA NAN: Zargin ba shi mukami a DPR: Hadimin Buhari da hukumar sun magantu
DUBA NAN: Jerin wadanda suka rike mukamin shugaban hukumar EFCC a tarihin Najeriya
A wani labarin kuwa, biyo bayan jita-jitan cewa APC na shirin janyo wani babba jiki don 2023, shugabannin jam'iyyar adawa ta Peoples Democratic Party PDP, sun kai ziyara ga tsohon shugaban kasa, Goodluck Jonathan.
Kwamitin sulhu na musamman karkashin jagorancin tsohon shugaban majalisar dattawa, Bukola Saraki, ne suka kai masa wannan ziyara.
A bara, jam'iyyar PDP ta kafa kwamiti na musamman domin sulhu tsakanin 'yayanta.
Goodluck Jonathan ya ce har yanzu yana nan a PDP inda ya ce "jam'iyyar tana tafiya tare da kowa."
Asali: Legit.ng