COVID-19: NLC za ta bi kadin karbawa ma'aikatan lafiya da suka mutu inshora

COVID-19: NLC za ta bi kadin karbawa ma'aikatan lafiya da suka mutu inshora

- Kungiyar kwadago ta sha alwashin bin kadin kudin inshoran ma'aikatan lafiyar da suka mutu sakamakon COVID-19

- Kungiyar ta koka kan yadda ma'aikatan lafiyar suka rasa rayukansu a kan aiki ba tare da biyansu inshora ba

- Kungiyar ta yi alkawarin hada kai da ma'aikatar lafiyan don karba musu hakkinsu

Kungiyar Kwadago ta Najeriya (NLC), ta ce za ta yi aiki tare da kungiyar ma’aikatan jinya da ungozoma ta kasa (NANNM), don bin kadin inshorar ma’aikatan kiwon lafiyar da suka mutu a cutar ta COVID-19, Vanguard News ta ruwaito.

Shugaban NLC, Mista Ayuba Wabba, ya yi wannan alƙawarin ne a taron kwana biyar na 7th Quadrennial National Delegates Conference na NANNM, a Abuja ranar Talata.

Ya ce: “Za mu yi aiki tare da ku don sanin adadin wadanda suka mutu don bin diddigin abin da suka yi alkawari a matsayin inshorar COVID-19.

KU KARANTA: Fulani na da 'yancin zama a Ondo, in ji sarakunan gargajiya a Ondo

COVID-19: NLC za ta bi kadin karbawa ma'aikacin lafiya da suka mutu inshora
COVID-19: NLC za ta bi kadin karbawa ma'aikacin lafiya da suka mutu inshora Hoto: This Day
Asali: UGC

“An fada mana cewa ma’aikatan lafiya 800 sun kamu da cutar COVID-19.

“Ma’aikatan kiwon lafiya a duniya suna da damar samun alawus na hadari don karfafa musu gwiwa su yi aiki, wasu kasashe suna yin irin wannan 50% cikin 100%.

“Ina sane da cewa a zango na biyu, akwai alawus-alawus da yawa da ba a biya ba; Ina kira ga gwamnati da ta mutunta fahimtar da muka cimma a zahiri. ''

KU KARANTA: Mata sun cancanci yabo ko don zaman gida da suke yi, Jarumar Nollywood

A wani labarin, Kasar Amurka ta bayar da gudummawar wani katafaren asibitin da zai taimakawa Najeriya wajen killace masu COVID-19, HumAngle ta ruwaito.

An bayar da gudummawar wurin ga Ma'aikatar Lafiya daga Ofishin Tsaro na Amurka reshen Afrika, tare da tallafin USAID, Cibiyar Kula da Cututtuka (CDC) da Walter Reed Army Institute of Research (WRAIR).

Mary Beth Leonard, Jakadiyar Amurka a Najeriya, tare da Olorunnimbe Mamora, karamin Ministan Lafiya, sun bude asibitin a ranar 22 ga Janairu a Cibiyar Kiwon Lafiya ta Tarayya da ke Jabi, Abuja, in ji Ofishin Jakadancin na Amurka a ranar Litinin.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel