Mata sun cancanci yabo ko don zaman gida da suke yi, Jarumar Nollywood
- Wata jarumar fina-finan Najeriya ta bayyana ra'ayinta kan yadda ya kamata a ga muhimmancin mata
- Jarumar ta kalubalanci al'umma da cewa ya kamata su yabawa mata kasancewarsu iyaye
- Ta bayyana zaman gidan da mata ke yi babban aiki ne da ba kowa ne zai iya yi ba
Jarumar Nollywood kuma ‘yar kasuwa, Mary Njoku ta ce mata sun cancanci yabo saboda kasancewar su matan gida dan kuwa aikin ba mai sauki bane, Daily Trust ta ruwaito.
Shahararriyar 'yar fim din ta bayyana hakan ne ta shafin ta na Instagram.
Njoku ta ce matan da suka bar burinsu na ƙuruciya don gina gida domin mazajensu su mayar da hankali ga burinsu sun cancanci yabo.
“Ya ku maza, zama uwa daya daga cikin mafarkin da mace take da shi ne. Kuma idan ta gama zama matar gida, ta sadaukar da komai a kanku.
KU KARANTA: Likitoci 3 sun mutu, 53 suna fama da Covid-19 a Kano
Jarumar ta bayyana irin wannan dabi’a daga mata a matsayin abu mafi wahala da za su yi, inda ta kara da cewa ya fi sauki fita neman kudi fiye da zama uwar gida.
“Aiki ne mafi wahala. Ya fi sauƙi fita da neman kuɗi fiye da kasancewa cikakkiyar matar gida, ku yarda da maganata saboda na dandana duka biyu.
Njoku ita ce fitacciyar yar wasan Najeriya kuma mai shirya fina-finai, ta shahara da shiryawa da kuma fitowa a fim din wasan kwaikwayo na shekarar 2015: "Thy Be Be Done ''.
Tana daya daga cikin jarumai mata da suka fi kwazo a Nollywood kuma aikinta a masana'antar fim sun sanya ta zama mai karfin fada aji da kuma daukaka a fim.
Jarumar, mai 'ya'ya uku, ta yi aure ne a shekarar 2012 da wani dan kasuwar Najeriya kuma wanda ya kirkiro Irokotv, Mista Jason Njoku.
KU KARANTA: Kadarorin da aka kona min sun kai miliyan N50m, in ji Sunday Igboho
A wani labarin, Kaftin din Super Eagles Ahmed Musa na shirin komawa kungiyar kwallon kafa ta West Bromwich Albion masu buga Premier a kan yarjejeniyar wani gajeren lokaci.
Dan wasan mai shekaru 28 bai kasance a wata kungiyar kwallon kafa ba tun lokacin da ya bar Al Nassr a cikin Oktoba 2020, The Punch ta ruwaito.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng