'Yan sanda sun cafke wani dan damfara mai ikirarin shi jami'in EFCC ne a Abuja

'Yan sanda sun cafke wani dan damfara mai ikirarin shi jami'in EFCC ne a Abuja

- 'Yan sanda sun samu nasarar kame wani bata-gari da ke amfani da sunansu wajen aikata laifuka

- Mutumin ya kasance yana karyar shi dan sanda ne a wani lokacin kuwa yace shi jami'in EFCC ne

- Wanda ake zargin an kame shi dauke da ankwa, takardun izinin kamu da sauran abubuwan 'yan sanda

Jami’an ‘yan sanda da ke reshen Mabushi na babban ofishin 'yan sanda na Babban Birnin Tarayya (FCT), Abuja sun cafke wani Mohammed Abdulrahman da ake zargi da yin karyar a matsayin Sufeto Janar na ‘yan sanda.

Hakazalika ana zarginsa da ikirarin cewa shi jami’in Hukumar Yaki da Yiwa Tattalin Arzikin Kasa Ta’annati EFCC, Nigerian Tribune ta ruwaito.

Wannan ya na kunshe ne a cikin wata sanarwa da kakakin rundunar, ASP ya bayar ga manema labarai a ranar Talata a Abuja. Mariam Yusuf.

PPRO ya bayyana cewa, wanda ake zargin wanda jami'an 'yan sanda suka kama a Mabushi bayan wani bayani da aka samu ya shahara da damfarar mutane da kuma kai musu hari ta hanyar nuna kansa a matsayin dan sanda.

KU KARANTA: Sojoji sun kashe 'yan bindiga 35 a Zamfara da Katsina

'Yan sanda sun cafke wani dan damfara mai ikirarin shi jami'in EFCC ne a Abuja
'Yan sanda sun cafke wani dan damfara mai ikirarin shi jami'in EFCC ne a Abuja Hoto: Nigerian Tribune
Asali: UGC

A cewar Yusuf an samu katunan ba da izinin kamu guda biyu, da sarka guda daya, da fesa hawaye guda daya, da bakar bel guda daya, da jan fez cap daya, da adda daya da kuma Toyota Camry bakar launi mai lamba kamar haka: AGL 541 ET.

PPRO ya bayyana cewa, Kwamishinan ‘yan sanda na rundunar, CP Bala Ciroma, ya bukaci jama’ar gari da su kai rahoton faruwar abubuwan da ba su dace ba da masu aikata miyagun laifuka a muhallin su zuwa ga rundunar‘ yan sanda mafi kusa.

KU KARANTA: Ana zargin Wani Bawan Allah da Kashe Matarsa A Kasar Italia

A wani labarin, Hukumar Kula da Abinci da Magunguna ta Kasa (NAFDAC) a ranar Juma’a ta bayyana cewa ba ta amince da duk wani rigakafin COVID-19 ba, The Nation ta ruwaito.

Ta yi gargadin alluran rigakafin bogi sun fara yawo a cikin kasar, inda ta yi kira ga jama'a da kar su sayi irin wadannan magunguna domin suna iya haifar da cututtuka irin na COVID-19 kuma za su iya haifar da mutuwa.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel