Gwamnatin jihar Kano za ta nada jami'an ladabtarwa na COVID-19
- Gwamnatin jihar Kano ta bayyana cewa za ta kaddamar jami'an kula da dokokin Korona
- Gwamnatin ta bayyana jami'an tsaro, 'yan banga da sauran kungiyoyi masu zaman kansu ne zasu kasance cikin shirin
- Gwamnan jihar ya yabawa masu makarantu masu zaman kansu don hadin kai da suka bayar na kiyaye dokar Korona
Gwamnatin Jihar Kano na shirin nada jami'an COVID- 19 don aiwatar da ladabtarwa kan tsaro, Gwamna Abdullahi Ganduje, ya sanar a ranar Asabar a Kano, The Nation ta ruwaito.
Ganduje ya shaidawa manema labarai cewa akwai bukatar a magance cutar ta COVID-19 duk yadda za a yi, saboda an gano rashin bin ka’idoji na kare lafiya a matsayin babban kalubale na dakile yaduwar cutar.
Ganduje ya ce gwamnatin jihar ta gudanar da taro da hukumomin da abin ya shafa domin nemo wani samfuri kan yadda za a aiwatar da wannan aiki.
KU KARANTA: Sabuwar jam'iyyar siyasa mai karfi na nan zuwa, in ji Okorocha
“Ba da jimawa ba za a fara aiwatar dokar bin ka'idoji na COVID-19 a jihar. Ya kamata mutane su kiyaye don lafiyar 'yan kasa,” inji shi.
Ya kara da cewa: "Kwamitin da ke aiki a kan COVID-19 ya yi taro da jami'an tsaro don fara aiwatar da shi don tabbatar da cewa al'umma suna yin biyayya ga kyakkyawan sakamako."
Gwamnan ya ce wadanda za su ci kasance cikin shirin sun hada da hukumomin tsaro, ‘yan banga da kuma kungiyoyi masu zaman kansu.
Ya roki kafafen yada labarai su ci gaba da fadakar da jama’a illolin wannan annoba.
"Muna matukar farin ciki cewa kuna ba da hadin kai ga gwamnatin jihar a wannan yakin," in ji shi.
Gwamnan, wanda kuma ya gana da masu mallakar makarantu masu zaman kansu, ya bukace su da su ba da hadin kai ga kokarin da gwamnati ke yi na dakile matsalar a makarantun su.
Ganduje ya yabawa masu makarantun kan hadin kan da suka bayar.
A wani labarin, Wata tawagar masu bincike a Jami'ar Ilorin (UNILORIN) sun gano karfin Bromelain wanda aka samo daga 'ya'yan itacen abarba don rage karfin kwayar cutar COVID-19, Vanguard ta ruwaito.
A cewar Jami'ar Ilorin a wata sanarwa da aka bayar a ranar Litinin, binciken ya kasance tare da Farfesa Bamidele Owoeye, Shugaban, Sashin Ilimin Kimiyyar Jiki, da Mista Ahmed Bakare, dalibin PhD a jami'ar.
KU KARANTA: 'Yan damfara da sunan COVID-19 sun bayyana a birnin Abuja, FCTA
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng