'Yan bindiga sun kashe mutum 8, sun kone gidaje a Zamfara
- 'Yan bindiga sun kai hari wasu kauyuka a Zamfara, sun kuma kashe mutane 8
- Shaidan gani da ido ya bayyana cewa 'yan kauyukan sunyi artabu da 'yan fashin kafin daga bisani suka bude wuta
- Hakazalika 'yan fashin sun dawo yayin da suka kone gidaje da yawa a kauyukan
'Yan bindiga sun sake kashe mutane takwas a kauyukan Dutsin Gari da Rayau da ke karamar hukumar Maru a jihar Zamfara a wani sabon hari.
Wani shaidar gani da ido, Malam Ibro Mamman ya zanta da wakilin The Punch ya ce ‘yan fashin a kan babura sun mamaye kauyen Dutsin Gari a daren jiya da niyyar yin garkuwa da wasu mutane amma mazauna garin sun fuskance su gaba daya.
A cewarsa, mazauna kauyen sun gwabza da 'yan fashin a wani kazamin fada wanda ya dauki tsawon awanni.
KU KARANTA: Sabuwar jam'iyyar siyasa mai karfi na nan zuwa, in ji Okorocha
Mamman ya ce, “Lokacin da 'yan fashin suka fahimci cewa ba za su iya yin nasara a cikin mummunan aikin nasu ba, sai suka bude wuta suka kashe mutane shida, suka ji wa da yawa rauni kafin su koma wani kauye da ke kusa da ake kira Rayau.
“A Kauyen Rayau, 'yan fashin sun kuma fuskanci irin wannan kalubale daga mazauna kauyen wadanda a shirye suke da karbar rahoton abin da ya faru a kauyen Dutsin Gari.
“Mazauna kauyen sun fito da yawa sun yi artabu da‘ yan fashin inda biyu daga cikin mazauna garin suka rasa rayukansu sannan ‘yan bindigar suka tafi ba tare da sun kame kowa ba,” in ji Mamman
Mamman ya kuma ce ‘yan fashin sun dawo kauyukan biyu da sanyin safiyar yau ne kawai don gano cewa mutane da yawa sun gudu zuwa garin Kanoma saboda tsoron ramuwar gayya.
A cewarsa, fusatattun yan fashin sun bankawa gidaje da yawa wuta sannan suka tafi da dabbobi.
KU KARANTA: Wasu masu bincike a UNILORIN sun ba da shawarar amfani da abarba don magance COVID-19
A wani labarin, Sojojin Operation Hadarin Daji sun fatattaki wasu 'yan fashi 35 tare da kame wasu abokan aikinsu a fafatawa daban-daban a Zamfara da Jihar Katsina, inji hedkwatar tsaro, The Nation ta ruwaito.
Mai Gudanarwa, Ayyukan Watsa Labarai na Tsaro, Maj.-Gen. John Enenche, ya bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa a ranar Litinin.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng