Kuma dai: Sama da mutane 1000 sun kamu da cutar Korona ranar sabuwar shekara

Kuma dai: Sama da mutane 1000 sun kamu da cutar Korona ranar sabuwar shekara

- Tun da aka samu ranar Litinin an dan samu sauki, adadin masu kamuwa da Korona ya karu

- A ranar karshen shekaran 2020, mutane 1031 ne suka kamu da cutar

- Har wa yau Najeriya bata sayo rigakafin Korona daga kasar Amurka da Ingila ba

Mutane 1074 kwayar cutar ta harba a fadin Nigeria a ranar Juma'a, 1 ga watan Junairu 2021, kamar yadda ya ke a sakon sanar da alkaluman sabbin mutane da cutar ke kamawa wanda NCDC ta saba fitarwa kullum.

Adadin da aka samu ranar Juma'a ya kai jimillan wadanda suka kamu da cutar 88,587 a Najeriya.

Daga cikin kimanin mutane 90,000 da suka kamu, an sallami 74,373 yayinda 1294 suka rigamu gidan gaskiya.

Wani sabon nauyin cutar Korona da ya samo asali daga Ingila ya shigo Najeriya makonnin bayan nan.

Kuma dai: Sama da mutane 1000 sun kamu da cutar Korona ranar sabuwar shekara
Kuma dai: Sama da mutane 1000 sun kamu da cutar Korona ranar sabuwar shekara Hoto: @NCDCgov
Asali: Twitter

Ga jerin jiha-jiha:

Lagos-642

Kaduna-92

Rivers-78

FCT-66

Gombe-66

Kano-35

Ogun-31

Katsina-22

Plateau-20

Abia-7

Niger-4

Oyo-4

Akwa Ibom-3

Delta-2

Osun-2

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel