FRSC ta umarci jami'anta da su koma kan tituna
- Kakakin rundunar hukumar FRSC, Bisi Kazeem ya sanar da yadda shugaban hukumar ya umarci duk wani jami'insu da cigaba da aiki
- Ya ce duk da sata, kone-kone da asarar dukiyoyin hukumar da bata-gari suka yi a jihohi daban-daban, ya umarci jami'an da su cigaba da kula da rayukan al'umma
- Hakan ya biyo bayan mummunan hatsarin da aka tafka a jihar Enugu, inda cikin mutane 56, 21 suka rasa rayukansu take-yanke
A wata takarda ta ranar Juma'a, Bisi Kazeem, Kakakin hukumar FRSC yace shugaban hukumar, Boboye Oyeyemi, ya bayar da umarni, inda yace jami'an FRSC su cigaba ta kula da tituna yadda ya dace.
Ya bayar da wannan umarnin ne bayan mutane 21 sun rasa rayukansu bayan wata babbar mota ta murkushe wata motar 'yan makaranta a jihar Enugu, The Cable ta ruwaito.
"Wadanda mummunan hatsarin jihar Enugu ya ritsa dasu, cikin mutane 56, 21 sun rasa rayukansu," a cewarsa.
"Hatsarin ya faru ne a kan kwanar Nkwo/Mmaku, kusa da tsohon titin Enugu/Okigwe a daidai karfe 4 na yamma a ranar Laraba, 28 ga watan Oktoba, 2020, tsakanin wata mota kirar Marsandi (ENU 811KU) dauke da yara 'yan makaranta da wata babbar mota Flatbed Mack Truck (KPP 247 XA)."
A cewarsa, "Hatsarin ya faru ne saboda matsalar birkin mota.
"Duk da hare-haren da bata-gari suka kai wa ofisoshin FRSC, inda suka lalata wasu abubuwa, suka saci wasu suka kuma kona wasu. Duk da haka ma'aikatan sun cigaba da ayyukan taimakon al'umma don kulawa da rayukan al'umma."
Kazeem yace Oyeyemi ya umarci duk wasu jami'an FRSC da su yi iyakar kokarinsu wurin kawo tallafi a tituna don kiyaye rayuka da dukiyoyin al'umma.
KU KARANTA: Dakarun soji sun halaka 'yan Boko Haram 13 a mako daya a Borno - DHQ
KU KARANTA: Saurayi ya biya wa budurwa 432,000 a mashaya, ta ki sauraronsa kuma ta bi wani saurayi
A wani labari na daban, gwamnati ta kafa kungiyar bincike a kan kisan gillar da ake zargin sojoji sun yi wa masu zanga-zangar SARS da aka rushe, inda suka kai ziyara asibitin sojoji da ke Falomo, wurin Ikoyi a jihar Legas.
Da farko an hana masu binciken shiga harabar asibitin na tsawon mintuna 30. Bayan an barsu sun shiga harabar, an kai su wurin da aka ce asibitin sojoji ne.
Masu binciken sun shiga har bayan asibitin, wuraren wani kango.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng