Sanwo-Olu ya fusata da rikicin kabilanci, ya yi tsokaci mai zafi

Sanwo-Olu ya fusata da rikicin kabilanci, ya yi tsokaci mai zafi

- Gwamnan jihar Legas, Sanwo-Olu, ya kai ziyara Fagba da ke wurin Ifako-Ijaiye, don jajanta wa wadanda asara ta hau kansu sakamakon wani rikici

- Rikicin ya barke tsakanin Hausawa da Yarabawa mazauna yankin, wanda ya ja asarar dukiyoyi masu yawa

- Gwamnan ya lashi takobin hukunta duk wanda ya gano yana da hannu a fadan, kuma zai yi kokarin biyan duk asarorin da aka tafka

Gwamnan jihar Legas, Babajide Sanwo-Olu, ya yi takaicin faruwar wani rikici da ya barke tsakanin Yarabawa da Hausawa a Fagba, wuraren Ifako-Ijaiye da ke jihar.

Bayan Sanwo-Olu ya kai ziyara wuraren ne a ranar Talata, ya lashi takobin hukunta duk wadanda ya gano suna da hannu a cikin rigimar, The Punch ta wallafa.

Ya tabbatar wa da mazauna wurin, wadanda rikicin ya shafa cewa zai share hawayensu.

Gwamnan da ya samu rakon mataimakinsa, Dr Obafemi Hamzat, sakataren gwamnatin jihar, Folasade Jaji, mai bai wa gwamnan shawara a harkar ilimi, Tokumbo Wahab da shugaban ma'aikata, Hakeem Muri-Okunola.

A cewarsa, "Irin asarar da na gani a wurin nan ta kazanta. Don haka za mu fara bincike take-yanke, a kan lamarin. Shugabannin unguwannin za su zauna su rubuta sunayen wadanda aka barnatar wa da dukiya.

"Muna so mu yi amfani da wannan damar wurin fadakar da bata-gari da ke kusa, don sannu a hankali za mu gano su.

"Idan mutum ya san bashi da wani aikin yi ko kuma yana cikin wadanda suka assasa rikicinnan, wannan ne jan kunne na karshe."

Ya kara da cewa, "Gwamnati za ta yi bakin kokarinta wurin biyan asarar, kuma masu shaguna su ji tsoron Allah yayin rubuta asarorinsu."

KU KARANTA: Rundunar soji ta halaka 'yan ta'adda 22, ta rasa zakakuran soji 5

Sanwo-Olu ya fusata sa rikicin kabilanci, ya yi tsokaci ma zafi
Sanwo-Olu ya fusata sa rikicin kabilanci, ya yi tsokaci ma zafi. Hoto daga @MobilePunch
Asali: Twitter

KU KARANTA: Da duminsa: Buhari ya sabunta nadin shugaban INEC, Farfesa Mahmood Yakubu

A wani labari na daban, 'yan sandan jihar Cross River sun sanar da kama Johnson Richard-Inem a ranar Litinin, ana zarginsa da kirkirar dabarar satar dukiyoyin gwamnati da wulakanta su ranar 24 ga watan Oktoba a Calabar International Conference Centre.

Hukumar ta bayyana yadda aka amso fiye da kujerun alfarma 1000, shimfidu na alfarma da sauran tsadaddun abubuwa daga hannunsa.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel