Wanda ya ci ya amayar: Gwamnatin Kaduna ta fara bi gida gida neman kayan COVID-19

Wanda ya ci ya amayar: Gwamnatin Kaduna ta fara bi gida gida neman kayan COVID-19

- Gwamnatin jihar Kaduna ta fara bi gida gida domin gano kayayyakin tallafin COVID-19 da aka sace a fadin jihar

- Nasir El-Rufai, gwamnan jihar Kaduna, ya tabbatar da wannan atisayen a shafinsa na Twitter, yana mai cewa, ba za a ragawa kowa ba

- Rundunar 'yan sanda tare da sauran jami'an tsaro ne za su fara wannan atisayen binciken gida gida don gano kayan

Gwamnatin jihar Kaduna ta fara bi gida gida domin gano kayayyakin tallafin COVID-19 da aka sace a dakin ajiyar kayan da ke wasu garuruwa na jihar.

Rundunar 'yan sanda tare da sauran jami'an tsaro ne za su fara wannan atisayen binciken gida gida don gano kayan tare da cafke wadanda aka kama da laifin satar su.

Nasir El-Rufai, gwamnan jihar Kaduna, ya tabbatar da wannan atisayen a shafinsa na Twitter a ranar Talata.

KARANTA WANNAN: Masu garkuwa sun kashe Kanal a rundunar soji bayan karbar kudin fansa N10m

Wanda ya ci ya amayar: Gwamnatin Kaduna ta fara bi gida gida neman kayan COVID-19
Wanda ya ci ya amayar: Gwamnatin Kaduna ta fara bi gida gida neman kayan COVID-19 - @thecableng
Asali: Twitter

Ya zuwa yanzu, rahotanni suna ta bayyana yadda bata gari ke ci gaba da fasa shaguna da dakin ajiyar kayan tallafi da ma na 'yan kasuwa, inda suke wawushe komai.

Ofishin hukumar kula da abinci da magunguna ta kasa NAFDAC, a jihar Kaduna, na daga cikin wuraren da bata garin suka kaiwa farmaki a jihar.

Baya ga satar kofofi da kayan ofis ofis, bata garin sun yi awan gaba da "masu hatsari kuma miyagun" magunguna, a cewar gwamnatin jihar.

A yayin da ya ke karin haske a wani jawabin, El-Rufai ya ce gwamnatinsa ta yanke hukuncin hukunta duk wanda ya saci kayan gwamnati ko na jama'a.

Ya ce gwamnati ba za ta lamunci sata da lalata kaya a jihar ba.

KARANTA WANNAN: Yadda miji da mata suka azabtar da karamar yarinya saboda alawar N10

A wani labarin, Gwamnatin tarayya na duba yiyuwar kai wa jamhuriyar Chadi wutar lantarki, biyo bayan bukatar hakan da makwabciyar kasar ta gabatar.

Kamfanin rarraba wutar lantarki mallakin gwamnati ya bayyana hakan a ranar Lahadi a taron da aka gudanar makon da ya gabata don duba yiyuwar kai wa Chadi wutar lantarki.

A halin yanzu Nigeria na da karfin wuta tsakanin 3,000MW zuwa 4,500MW, kuma ko a yanzu, Nigeria na kai wutar lantarki ga jamhuriyyar Niger, Benin da Togo.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel