Dalla-dalla: Abinda Buratai ya sanar da kwamandojinsa a taronsu na ranar Litinin

Dalla-dalla: Abinda Buratai ya sanar da kwamandojinsa a taronsu na ranar Litinin

- Shugaban rundunar sojin kasa, Laftanal janar Tukur Buratai, ya umarci sojoji da su tabbatar da zaman lafiya a Najeriya

- Ya sanar da hakan ne a wani taro da yayi da manyan shugabannin sojojin kasa a ranar Litinin, 26 ga watan Oktoba a Abuja

- Ya kara da cewa, akwai bata-gari da dama da suke jiran karamin rikici ya auku don su rurar da wutar tashin hankali

Shugaban rundunar sojin kasa, Laftanal janar Tukur Buratai, ya yi wani taro da manyan shugabannin rundunar soji, duk wasu GOC da kwamandojin filin daga.

Kamar yadda The Nation suka tattaro bayanai akan taron da akayi a hedkwatar tsaro a ranar Litinin, 26 ga watan Oktoba.

Kamar yadda jaridar ta ruwaito, Buratai ya ce wa manyan jami'an soji su tabbatar sun zama masu juriya, don hargitsa Najeriya ba nasu bane.

Ya ce wajibi ne sojojin Najeriya su tabbatar da sun samar da kwanciyar hankali a kasa, don mulkin farar hula ne yafi kowanne salon mulki samar da zaman lafiya a Najeriya.

Ya kara da cewa, "Ba za mu bari wasu mutane su yi amfani da karfinsu wurin raba mana kasa ba, ko kuma su rura mana wutar tashin hankali ba."

Buratai ya ce ba zai bayar da wata dama da wani zai ci amanar kasa ba. Kuma ya umarcesu da su tabbatar sun sanar da na kasa dasu.

Ya ce daga ganin wannan zangar-zangar EndSARS din, bata-gari na samun dama za su yi kokarin raba Najeriya.

Yace yana sane da shirin wasu mutane na hada tuggun tayar da hankula, shiyasa suka dauki matakan da suka dace.

KU KARANTA: Tallafin korona: Wasu jihohi sun fito da kayan abinci, sun fara raba wa talakawa

Dalla-dalla: Abinda Buratai ya sanar da kwamandojinsa a taronsu na ranar Litinin
Dalla-dalla: Abinda Buratai ya sanar da kwamandojinsa a taronsu na ranar Litinin. Hoto daga @TheNation
Asali: Twitter

KU KARANTA: Da duminsa: Ahmed Musa ya bar kungiyar Al Nassr da ke Saudi Arabia

A wani labari na daban, Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya roki iyaye da su koro yaransu da duk wasu kayan alatu da suka koma da shi gida, wanda sun san ba za su iya siya da kansu ba, The Cable ta wallafa.

Ya sanar da hakan ne bayan zanga-zangar EndSARS ta tsawon sati guda, wacce ta ja bata-gari suka yi ta wadaka da dukiyar gwamnati da ta al'umma a fadin kasa.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel