Da duminsa: Bata-gari sun bankawa ofishin 'yan sanda wuta, sun kone ababen hawa a Ibadan

Da duminsa: Bata-gari sun bankawa ofishin 'yan sanda wuta, sun kone ababen hawa a Ibadan

- Wasu matasa da ake zargin bata-gari ne sun banka wa ofishin 'yan sanda wuta a Ibadan

- Hakan ta faru ne bayan 'yan sandan sun yi yunkurin tarwatsa masu zanga-zanga

- Basu tsaya a nan ba, sun banka wa dukkan ababen hawan da ke farfajiyar ofishin wuta

Wasu fusatattun matasa a garin Ibadan da ke jihar Oyo, sun banka wa ofishin 'yan sanda da ke Ojoo wuta.

Ganau ba jiyau ba sun sanar da The Cable cewa rikicin ya fara ne bayan 'yan sanda sun yi yunkurin watsa masu zanga-zanga.

Wasu da ake zargin 'yan daba ne a cikin gayyar masu zanga-zangar sun dinga jifan 'yan sandan da duwatsu wanda hakan yasa 'yan sandan suka bude wuta.

Fusatattun masu zanga-zangar sun fi 'yan sandan yawa kuma sun shige cikin ofishin inda suka banka masa wuta.

Da yawa daga cikin ababen hawan da ke farfajiyar ofishin 'yan sanda an kone su.

Karin bayani na nan tafe...

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel