Saurayi ya yi wuff da wata budurwa bayan budurwarsa na dauke da cikinsa wata 7

Saurayi ya yi wuff da wata budurwa bayan budurwarsa na dauke da cikinsa wata 7

- Wata mata 'yar Uganda ta shiga cikin mummunan tashin hankali bayan sanin cewa saurayin da take da ciki dashi ya yi aure

- Tace sun yi nisa a soyayyarsu a 2018, har ta samu ciki, ta tambayeshi idan yana so ta haife cikin, ya amince da hakan, ashe yaudara na tafe

- Bayan ta samu cikin da watanni 7 ya auri wata matar, sai da taga hotunan bikinsa da amaryarsa ta shiga tashin hankali

Wata mata 'yar Uganda ta shiga cikin mummunan tashin hankali bayan sanin cewa saurayin da take da cikinsa ya aura wata.

Wata mata mai da daya ta sanar da Mywedding.co.ug cewa sun fara soyayya da wani mutum mai suna Norman a 2008, ranar da suka fara haduwa sai soyayyar juna ta ratsa zuciyoyinsu.

Matar tace a ranta tayi yakinin cewa soyayyar su wata rana zata kai ga aure.

A lokacin da ta gano tana da ciki da Norman, tayi farin ciki matuka, saboda zata hada zuri'a dashi.

Masoyin nata, Norman, yana aikin gwamnati kuma yana tafiye-tafiye zuwa garuruwa daban-daban, don haka basu samun damar ganin juna sosai, sai dai su na yawan magana ta waya.

Hankalinta ya yi matukar tashi bayan ta fahimci cewa yana tarayya da wata mata. Tace bayan ta sanar da Norman tanada juna biyu ya amince ta haife jaririn.

KU KARANTA: Neymar: Dan wasan kwallon kafan da ya mallaki motoci na N2bn (Hotuna da Bidiyo)

Saurayi ya yi wuff da wata budurwa bayan budurwarsa na dauke da cikinsa wata 7
Saurayi ya yi wuff da wata budurwa bayan budurwarsa na dauke da cikinsa wata 7. Hoto daga Mywedding.co.ug
Asali: UGC

Tace ta fara zargin wani abu a lokacin da aminiyarta ke tambayarta idan ya yarda ta haife jaririn, ashe tana da ciki wata 7 yayi aurensa. Bata yarda da hakan ba sai bayan taga hotunan bikin.

KU KARANTA: Da duminsa: Buhari ya kori shugaban hukumar hakkin mallaka

A wani labari na daban, an dakatar da dalibai 20 'yan aji 4 da ke babbar makarantar sakandire ta Loreto a Zimbabwe sakamakon kamasu da laifin lalata da juna a watan Yuli.

Da yake makarantar ta maza da mata ce, an kama daliban tsirara suna lalata a inda yara matan ke kwana na makarantar da ke Silobela, yayin da suke shirin fara jarabawar watan Yuni zuwa Yuli.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel