Manyan Mataki 2 da Suka Hargitsa Yan Najeriya da Tinubu Ke Ikirarin Gyara Ne
- Ministan Yaɗa Labarai, Mohammed Idris, ya bayyana mata a matsayin abokan hulɗa masu muhimmanci wajen bunƙasa Najeriya
- Idris ya ce cire tallafin man fetur da haɗa farashin canjin kuɗaɗen waje sun taimaka wajen samar da tubalin farfaɗo da tattalin arzikin ƙasar
- Ya buƙaci ƙungiyar Women of Influence for Tinubu 2027 ta ƙara wayar da kan jama’a domin fahimtar manufofin gwamnatin Tinubu
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Abuja - Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kan Ƙasa, Mohammed Idris, ya bayyana muhimmancin mata a shirye-shiryen gwamnati.
Idris ya bayyana mata a matsayin abokan hulɗa masu muhimmanci wajen bunƙasa Najeriya da inganta fahimtar manufofin gwamnati.

Source: Facebook
Idris ya bayyana hakan ne lokacin da ya karɓi Hauwa Ibrahim, mai jagorantar ƙungiyar Women of Influence for Tinubu 2027, wadda ta jagoranci tawagar ƙungiyar zuwa ma’aikatar a ziyarar girmamawa, cewar The Guardian.

Kara karanta wannan
Gwamnatin Tinubu ta ɗauko hanyar gyara, za a samu rangwamen tsadar rayuwar kwana 90
A cikin wata sanarwa, ministan ya bayyana cewa sauye-sauyen tattalin arziki da Shugaba Bola Tinubu ya ƙaddamar suna aza harsashin gina Najeriya mai ƙarfi, wadata da juriya ta fuskar tattalin arziki.
Ya ce:
“Shirin sauye-sauyen Shugaba Bola Ahmed Tinubu an tsara shi ne domin kai Najeriya ga wadata. Cire tallafin man fetur da haɗa farashin canjin kuɗaɗen waje matakai ne masu muhimmanci da suka zama dole domin daidaita tattalin arzikin ƙasar da sake tsara shi domin bunƙasa.”
Idris ya ƙara da cewa an ɗauki waɗannan matakai ne da gangan da kuma jajircewa domin magance tsofaffin matsalolin tattalin arziki, dawo da daidaiton kuɗaɗen gwamnati da samar da ƙarin damarmakin ci gaba mai ɗorewa.
A cewarsa, sauye-sauyen sun ƙara yawan kuɗaɗen da gwamnatin tarayya, jihohi da ƙananan hukumomi ke samu domin zuba jari a muhimman ababen more rayuwa, ayyukan yau da kullum da sauran abubuwan da ke shafar rayuwar ’yan Najeriya.

Source: Facebook
Minista ya sake kwantarwa yan Najeriya hankali
Ministan ya jaddada cewa duk da cewa sauye-sauyen sun buƙaci mutane su yi haƙuri da wasu matsaloli, amfaninsu na dogon lokaci zai ƙarfafa tattalin arzikin ƙasar tare da tabbatar da kyakkyawar makoma ga tsararraki masu zuwa.
Ya ce:
“Abu ne mai sauƙi ƙwarai a manta inda muka fito. Waɗannan matakai ne masu wahala, amma an ɗauke su ne domin amfanin ƙasarmu da wadata ga tsararraki masu zuwa.”
Idris ya buƙaci mambobin ƙungiyar su ƙara ƙoƙarin wayar da kan ’yan Najeriya, musamman a matakin ƙasa, ta hanyar bayyana manufofin gwamnati, dalilan ɗaukar matakan sauye-sauye da damarmakin ci gaban da suke samarwa.
Ya ce:
“Ina roƙonku da ku rinjayi sauran ’yan Najeriya domin su fahimci manufofin wannan gwamnati tare da tallafa mata yayin da take ci gaba da ƙoƙarin sake fasalin ƙasarmu.”
Minista ya magantu kan dawo da tallafi
Mun ba ku labarin cewa Ministan Yaɗa Labarai, Mohammed Idris, ya ce rangwamen man fetur na NNPC na kwanaki 30 ba komawa tallafin mai ba ne.
Ya bayyana cewa NNPC ta amince da rage wasu ribar da take samu domin rage wa ’yan Najeriya raɗaɗin tsadar man fetur.
Ministan ya ce gwamnatin Tinubu na ci gaba da gyare-gyaren tattalin arziki, tare da ƙara samar da makamashi mai araha.
Asali: Legit.ng
