Yanzu yanzu: IGP ya gayyaci jami'an SARS Abuja domin ayi masu gwajin kwakwalwa

Yanzu yanzu: IGP ya gayyaci jami'an SARS Abuja domin ayi masu gwajin kwakwalwa

- IGP Mohammed Adamu ya umurci gaba daya jami'an SARS da su je shelkwatar rundunar da ke Abuja domin ayi masu gwajin kwakwalwa

- Za ayiwa jami'an gwajin kwakwalwar ne a shirye shiryen horas da su domin rarrabasu zuwa wasu sashe sashe na rundunar

- Haka zalika, an samar da sabon sashe a rundunar, na kwararrun jami'ai a sarrafa makamai da yaki (SWAT) kuma za a fara yi masu horo mako mai zuwa

Sifeta Janar na rundunar 'yan sanda, Mohammed Adamu a ranar Talata ya umurci gaba daya jami'an da ke a sashen dakile fashi da makami SARS da su je shelkwatar rundunar da ke Abuja.

Rahotanni sun bayyana cewa jami'an idan sun je Abuja, za ayi masu gwajin kwakwalwa a shirye shiryen yi masu horo don rarrabasu zuwa wasu sashe sashe na rundunar.

Da ya ke bayyana hakan a cikin wata sanarwa, Frank Mba, jami'in hulda da jama'a na rundunar, ya ce: "Sabon sashen tuntuba da bayar da shawarwari na rundunar (PCSU) zai gudanar da binciken kwakwalwar.

KARANTA WANNAN: Rundunar 'yan sandan Lagos ta kwace makamai daga hannun jami'an SARS

Yanzu yanzu: IGP ya gayyaci jami'an SARS Abuja domin ayi masu gwajin kwakwalwa
Yanzu yanzu: IGP ya gayyaci jami'an SARS Abuja domin ayi masu gwajin kwakwalwa - @vanguardngrnews
Asali: UGC

"Sashen zai kula da lamarin horaswa, binciken kwakwalwa da kuma bayar da shawarwari ga jami'an 'yan sanda da aka turasu ayyukan dakile ta'addanci."

Sashen, wanda ya ke jingine da bangaren kiwon lafiya na rundunar kuma karkashin kulawar jami'in lafiya, na da ma'aikatan kwakwalwa, ilimin rayuwa, likitanci, malaman addinai, jami'an hulda da jama'a da sauransu.

KARANTA WANNAN: Yan sanda sun kashe masu zanga zangar EndSARS guda 10 - Amnesty

A wani ci gaban, IGP ya samar da sashen jami'an da suka kware a sarrafa makamai da fada (SWAT) da zai cike gurbin korarren sashen jami'an SARS.

Mambobin wannan sabon sashen za su samu horo da kuma jarabawar kwakwalwa domin tabbatar da cewa za su iya gudanar da wannan muhimmin aiki.

Za su fara samun horo a sansanonin horar da jami'an rundunar 'yan sanda daban daban da ke fadin kasar, a mako mai zuwa.

Za a horas da jami'an rundunar da ke a shiyyoyin Kudu maso Gabas da Kudu maso Kudu a sansanin horas da jami'an na Nonwa-Tai, jihar Rivers.

Haka zalika, za a horas da jami'an rundunar 'yan sandan shiyyar Arewa da Kudu maso Yamma a kwalejin horas da 'yan sandan sintiri da ke Ende, jihar Nasarawa da kuma wacce ke Ila-Orangun, jihar Osun.

A wani labarin, Kwamishinan 'yan sandan jihar Lagos, Hakeem Odumosu, ya ce bi umurnin Sifeta Janar na rundunar 'yan sanda, Mohammed Adamu, na ruguza sashen rundunar SARS.

Odumosu, wanda ya gana da wasu lauyoyi da suke zanga zanga kan cin zarafin da jami'an SARS ke yiwa jama'a, ya ce tuni aka kwace makamai daga hannun jami'an rundunar SARS.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel