Yan sanda sun kashe masu zanga zangar EndSARS guda 10 - Amnesty

Yan sanda sun kashe masu zanga zangar EndSARS guda 10 - Amnesty

Kungiyar Amnest International, ta ce rundunar 'yan sanda sun kashe mutane 10 da ke zanga zangar #EndSARS da aka fara ranar Alhamis.

Amnesty ta bayyana hakan ne a shafinta na Twitter a ranar Litinin.

Ta ce, "Ya zuwa yanzu, rundunar 'yan sandan Nigeria ta kashe akalla mutane 10 tun bayan da aka fara zanga zangar kawo karshen rundunar SARS a kasar.

KARANTA WANNAN: Sakon Atiku Abubakar ga matasan Nigeria bayan rushe rundunar FSARS

Yan sanda sun kashe masu zanga zangar EndSARS guda 10 - Amnesty
Yan sanda sun kashe masu zanga zangar EndSARS guda 10 - Amnesty - @MobilePunch
Asali: Twitter

A ranar Asabar, kamar yadda rahotanni suka bayyana, 'yan sanda a garin Ogbomosho, jihar Oyo, sun kashe wani matashi, Isiaq Jimoh, wanda ke cikin masu zanga zangar.

A ranar Litinin kuwa, an sake kashe wani mai zanga zangar a yankin Surulere, jihar Lagos.

KARANTA WANNAN: An tsige kakakin majalisar jihar Edo, Francis Okiye

A wani labarin kuma, shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya ce zai tabbata an dauki mataki kan gurbatattun jami'an SARS, ba tare da nuna sani ko sabo ba.

Shugaban kasar ya bayyana hakan a ranar Litinin a Abuja a yayin kaddamar da wani shirin shugaban kasa na mata, da zai samar da ayyuka ga matasa 774,000 a jihohi 36 na kasar.

Buhari ya kuma ce ruguza rundunar SARS, matakin farko ne na yin garambawul a rundunar 'yan sandan Nigeria karkashin gwamnatin sa.

A wani labarin, Tsohon mataimakin shugaban kasar Nigeria, Atiku Abubakar, a ranar Lahadi ya jinjinawa matasan Nigeria bisa jajurcewarsu na yakar zaluncin da rundunar 'yan sanda ke yi.

Atiku, ya nuna gamsuwarsa, kan yadda matasan kasar suka hurawa rundunar 'yan sanda wuta har sai da ta rushe sashen rundunar na FSARS da ke yaki da fashi da makami.

A cikin wata sanarwa daga hadiminsa ta fuskar watsa alabarai Paul Ibe a Abuja a ranar Lahadi, Mr Abubakar ya ce rushe SARS alama ce ta bin tsarin wadatar da 'yan Nigeria ta fuskar tsaro.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel