Magidanci ya saka wa bishiyarsa raga domin hana makwabta amfana da ita

Magidanci ya saka wa bishiyarsa raga domin hana makwabta amfana da ita

- Hotunan bishiyar 'ya'yan itacen da aka rufe da raga ya jawo cece-kuce a kafafen sada zumuntar zamani

- Wani mutum ya rufe bishiyarsa da raga saboda kada makwabtansa su tsinka 'ya'yan itacen bishiyar tasa

- Duk da rassan bishiyar sun fita har ta katanga, mai bishiyar ba zai so 'ya'yan itatun su sauka a gidan makwabtansa ba

Mutane da dama zasu so ace suna cin abinci da 'ya'yan itatu a gefensu, saboda abincin zai fi shiga.

Amma wanne dalili ne zai sa mai bishiya yayi kokarin hana makwabtansa sha daga 'ya'yan itacen gidansa?

Mutane sun yi ta mamaki, wasu kuma suna al'ajabin irin wannan bakar rowa, bayan ganin hoton wata bishiya rufe da raga.

Wata mata mai suna Janet Machuka, ta wallafa hoton wata bishiya dake rufe da raga, inda tayi tsokaci a kasa, tace "anya akwai irin waddanan makwabtan?"

Wani mutum, wanda ba zai iya jure ganin makwabtansa na shan 'ya'yan itacen bishiyarsa ba, ya rufe bishiyar da raga, duk da reshen bishiyar ya shiga makwabtansa.

Mutumin yayi iya kokarinsa na tabbatar da kusan duk 'ya'yan itacen suna cikin ragar.

Mutane da dama sun yi ta tsokaci akan hoton, inda wasu ke cewa son kansa yayi yawa, wasu kuma ke cewa in dai har makwabcinsu yayi makamancin hakan, sai sun yanke bishiyar.

KU KARANTA: Majalisar jihar Edo ta yi sabon kakaki, ya dakatar da tsohon kakakin

Magidanci ya saka wa bishiyarsa raga domin hana makwabta amfana da ita
Magidanci ya saka wa bishiyarsa raga domin hana makwabta amfana da ita. Hoto daga Janet Machuka
Asali: UGC

KU KARANTA: Bidiyo da hotunan budurwa ta garzaya wurin aikin saurayinta cikin shigar amare, ta bukaci a daura musu aure

A wani labari na daban, 'yan sanda sun balle kofar wani gida a Benin inda suka riski mutane 7 a mawuyacin hali.

Mutum 1 daga cikinsu ya rasu, 6 kuma suna asibiti. Ana zargin sun ci abinci sai suka kwanta, basu tashi washegari ba. Wani dan sanda ya sanar da jaridar Daily Trust cewa watakil hayakin janareto da suka kunna ne ya jawo wannan matsalar.

Al'amarin ya faru ne a gida mai lamba 40 akan titin Otete, kusa da layin masaka a Ogida quarters a cikin Benin City.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel