Bidiyo da hotunan budurwa ta garzaya wurin aikin saurayinta cikin shigar amare, ta bukaci a daura musu aure

Bidiyo da hotunan budurwa ta garzaya wurin aikin saurayinta cikin shigar amare, ta bukaci a daura musu aure

- Bidiyon wata mata 'yar Los Vegas ya karade shafukan sada zumuntar zamani, inda aka ga matar cikin shiga irin ta amare

- Matar ta biyo saurayinta har wurin aikinsa, tare da kawayenta da Fasto don a daura mata aure dashi take yanke

- A Bidiyon, ta nuna masa cewa matsawar yaki amincewa da tayin aurenta, to tabbas zata barshi har abada

Hankula sun karkata akan bidiyon wata mata da tayi shiga irin ta amare a Los Vegas.

A gefenta akwai kawayenta wadanda suka yi ado da wasu suturu masu kalar ruwan kasa, da takalma masu tsayi.

Matar, wadda ba'a bayyana sunanta ba ta matsa cewa sai ta ga saurayinta dake aiki a wani shago.

Tare da matar akwai Fasto, kuma tana rike da zoben daurin aure. Matar bata bukatar jin kalmar "a'a" daga bakin saurayin nata.

An nuna matar tana fuskantar saurayin nata, inda tace indai har yaki amincewa da tayin aurenta to tabbas zata rabu dashi.

Matar ta shayar da mutane da dama mamaki, a yadda ta dage kuma da alamun ta gama auna komai.

Saurayin yayi mamakin al'amarin, inda ya daura kansa akan cinyarsa saboda tsananin mamaki.

KU KARANTA: EndSARS: Fadar shugaban kasa ta bayyana abinda take yi a kan zanga-zanga

Budurwa ta garzaya wurin aikin saurayinta cikin shigar amare, ta bukaci a daura musu aure
Budurwa ta garzaya wurin aikin saurayinta cikin shigar amare, ta bukaci a daura musu aure. Hoto daga Boymom_ashley/TikTok
Asali: UGC

KU KARANTA: Ambaliyar ruwa: Rayuka 36 sun salwanta, mutum 470 sun rasa gidajensu

Budurwa ta garzaya wurin aikin saurayinta cikin shigar amare, ta bukaci a daura musu aure
Budurwa ta garzaya wurin aikin saurayinta cikin shigar amare, ta bukaci a daura musu aure. Hoto daga Boymom_ashley/TikTok
Asali: UGC

A wani labari na daban, a ranarJuma'a, 10 ga watan Oktoban 2020 ne sabon sarkin Zazzau, Alhaji Ahmed Nuhu Bamalli ya yi sallar Juma'a ta farko bayan nada shi da aka yi.

Gwamnan jihar kaduna, Malam Nasir El-Rufai ya nada Alhaji Ahmed Nuhu Bamalli a matsayin sabon Sarkin Zazzau na 19 bayan rasuwar Balaraben Dakta Shehu Idris.

Manyan masu sarauta a masarautar Zazzau sun yi mubaya'a ga sabon sarkin. Tun bayan nada sabon sarkin, ya shiga fadar masautar cike da murna tare da farin cikin sarautar da ta koma gidan Mallawa wacce ta barsu tun shekaru 100 da suka gabata.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel