Ba za mu rushe SARS ba - Kakakin NPF ya fadi muhimmancin jami'an rundunar
- 'Yan Najeriya na cigaba da nuna fushinsu tare da neman gwamnati ta soke rundunar 'yan sandan SARS da aka kafa domin yaki da fashi da makami
- Ma su neman a soke SARS su na zargin jami'an rundunar da aikata laifukan da aka kafasu domin su yaka
- A yayin da aka shiga rana ta biyu da fara gudanar da zanga-zanga a wasu jihohi, an samu barkewar rikici tsakanin jami'an tsaro da fararen hula
Frank Mba, mai magana da yawun rundunar ƴan-sanda, ya ce abune mawuyaci ƙungiyar da ta san abun da take yi ta nemi a kawo ƙarshen sashen hana fashi da makami (SARS).
Da yake magana game da zanga-zangar da ake gudanarwa a kan neman rushe sashen hana fashi da makami na rundunar yan sanda, Mba yace wasu daga cikin jami'an su na daga cikin masu yaƙi da ta'addanci da kuma fashi a arewacin Najeriya.
Da yake magana a gidan talabijin na Channels a ranar Juma'a, Mba ya ɗora laifin zangar-zangar a kan masu cin moriyar laifuka inda ya ce wasu daga cikin masu zanga-zangar masu cin moriyar laifukan ne.
"Idan har kiran a kawo karshen sashen hana sashen fashi da makami (SARS) manuniya ce ta gyara, zan faɗi cewa shugabancin rundunar ƴansanda a shirye yake da ya karɓi kiran.
''Sai dai kuma idan kiraye-kirayen na nufin a dakatar da sashen gabaɗaya, zan faɗa muku abune mayuwaci ga kowacce irin gwamnati da ta san abinda take yi ta yarda da hakan musamman idan aka yi la'akari da maƙudan kuɗaden da gwamnati ta zuba wajen bada horo da kuma ƙirkirar sashen, baya ga muhimmiyar rawa da sashen yake takawa.''

Asali: Twitter
''Magana ta gaskiya mun karɓi kiraye kiraye da kuma ƙorafi daga mutane musamman daga Maiduguri, Yobe da kuma sauran jihohin arewa inda jami'an SARS ke aiki tukuru wajen yaƙi da fashi da kuma ta'addancin kungiyar Boko Haram.
"Ma su ƙorafin sun bayyana cewa kawo karshen sashen ba shine mafita ba a garesu sakamakon gagarumar gudunmawar da jami'an ke bayarwa a yankin su musamman akan ƴanfashi, 'yan Boko Haram da sauran ƴanta'adda da kuma sauran masu muggan laifuka," a cewarsa.
Mba ya ce a yayin da wasu su ke damuwa game da ayyukan sashen rundunar SARS, ma su manyan laifuka na son a dakatar da sashen ne don buƙatar su cigaba da cin karen su babu babbaka.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayarku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng