Da duminsa: 'Yan majalisar nadin sarakuna 5 sun yi wa Bamalli mubaya'a

Da duminsa: 'Yan majalisar nadin sarakuna 5 sun yi wa Bamalli mubaya'a

- 'Yan majalisar sarakuna sun yi mubaya'a ga sabon Sarkin Zazzau, Ahmed Nuhu Bamalli, sun nuna cikakkiyar amincewarsu

- Ba su kadai bane wadanda suka bi sabon sarkin, hatta Yeriman Zazzau, Alhaji Munir Ja'afaru ya taya shi farin ciki

- Murna ta barke a cikin Farfajiyar fadar sarkin Zazzau, dama shekaru 100 kenan rabon da sarauta ta koma gidan Mallawa

'Yan majalisar nadin sarakunan Zazzau sun amince da zabar Ahmed Bamalli a matsayin sarkin Zazzau, babu dadewa da nada shi.

An nada Ahmed Nuhu Bamalli a matsayin sarkin Zazzau a ranar Laraba, 7 ga watan Oktoban 2020.

Bayan rasuwar Sarki Shehu Idris da yayi shekaru 45 a karagar mulki (1975-2020).

Jim kadan bayan Sakataran Gwamnatin jihar Kaduna ya isa fadar sarkin Zazzau da sanarwar nadin sabon sarkin, 'yan uwa da abokan arziki da al'ummar Zazzau suka yi ta tururuwar zuwa fada farin ciki.

KU KARANTA: Operation Kashe Mugu: NAF ta kaddamar da sabon shirin kawar da 'yan bindiga a Arewa

Da duminsa: 'Yan majalisar nadin sarakuna 5 sun yi Bamalli mubaya'a
Da duminsa: 'Yan majalisar nadin sarakuna 5 sun yi Bamalli mubaya'a. Hoto daga @GovKaduna
Asali: UGC

KU KARANTA: Iyalai 12,000 za su amfana da tallafin tsabar kudi a jihar Kano

Alhaji Munir Ja'afaru, Yeriman Zazzau kuma daya daga cikin manema kujerar ya isar da sokon taya murnarsa da kuma amincewarsa dari-bisa-dari da nadin, har yana cewa Allah ne ke bayar da mulki ga wanda yaso.

'Yan majalisar zaben sarkin sun hada da Limamin Kona; Sani Aliyu, Limamin Juma'a; Dalhat Kasim, Makama Karami; Mahmood Abbas, Fagacin Zazzau; Umar Mohammed da Wazirin Zazzau; Ibrahim Aminu.

Kamar yadda aka sani, masarautar Zazzau nada gidajen sarauta 4, sune Gidan Katsina, Barebari, Mallawa da kuma Fulani.

Sabon sarki, Ahmed Bamalli dan asalin gidan Mallawa ne, wanda a tarihi, shekaru 100 kenan rabon da sarauta ta koma gidan.

Tun bayan mutuwar kakansa, Alu Dan Sidi, sarki na 13 tun 1920.

A wani labari na daban, murna da shagali ya barke a garin Zazzau bayan da gwamnan jihar Kaduna ya bayyana Alhaji Ahmad Bamalli a matsayin Sarkin Zazzau na 19.

Bayan bada sanarwar, garin ya dinke da farin ciki da murna tare da kabbarori. Jama'a da dama sun dinga fatan alkhairi tare da taya sabon Sarkin Murna wannan karagar mai dumbin tarihi da ya haye.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel