Hotunan yadda aka tsananta tsaro a fadar sabon Sarkin Zazzau

Hotunan yadda aka tsananta tsaro a fadar sabon Sarkin Zazzau

- An tsananta matakan tsaro a farfajiyar fadar sabon Sarkin Zazzau, Sarki Ahmed Nuhu Bamalli

- Tun bayan nadin sarkin, jama'a ta ko ina suka yi ta kutsawa cikin fadar suna farin cikin nadin

- Sarkin shine na farko a tsatson Mallawa tun bayan rasuwar kakansa a shekaru 100

Bayan nadin sabon sarkin Zazzau, an tsananta tsaro a farfajiyar fadar sabon Sarkin Zazzau.

Gidan talabijin na Channels sun nuna yadda mutane suka yi ta kutsawa fadar suna murna.

Al'amarin ya biyo bayan nada Ahmed Nuhu Bamalli a matsayin sarkin Zazzau na 19 wanda Gwamna Nasir El-Rufai yayi.

Bamalli ya gaji marigayi sarki Shehu Idris wanda ya rasu a ranar 20 ga watan Satumba, 2020 bayan mulkar masarautar na shekaru 45.

Bamalli ne farkon sarki daga gidan mallawa tun bayan rasuwar kakansa, Sarki Dan Sidi a shekarar 1920.

Shekaru 100 kenan da rasuwarsa, sai wannan karon mulki ya dawo gidan mallawa.

Hotunan yadda aka tsananta tsaro a fadar sabon Sarkin Zazzau
Hotunan yadda aka tsananta tsaro a fadar sabon Sarkin Zazzau. Hoto daga @ChannelsTv
Asali: Twitter

KU KARANTA: Bayan musayar wuta, 'yan Boko Haram sun halaka jami'in JTF a Borno

A wani labarai na daban, murna da shagali ya barke a garin Zazzau bayan da gwamnan jihar Kaduna ya bayyana Alhaji Ahmad Bamalli a matsayin Sarkin Zazzau na 19. Bayan bada sanarwar, garin ya dinke da farin ciki da murna tare da kabbarori.

Jama'a da dama sun dinga fatan alkhairi tare da taya sabon Sarkin Murna wannan karagar mai dumbin tarihi da ya haye.

Idan za mu tuna, a a ranar 20 ga watan Satumban 2020 ne Allah ya yi wa balaraben Sarki, Alhaji Dakta Shehu Idirs rasuwa.

Ya rasu yana da shekaru 84 a duniya bayan kwashe shekaru 45 da yayi a karagar mulkin. Jama'a da dama sun yi cincirindo a fadar sarkin inda suka jira isowarsa sannan suka raka sa har ciki.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel