Buhari ya amince a bawa daliban da suka yi karatun NCE aiki, ya kara shekarun aikin malamai

Buhari ya amince a bawa daliban da suka yi karatun NCE aiki, ya kara shekarun aikin malamai

- A yanzu daliban da suke karatu a bangaren koyar da ilimi (NCE) za su samu aikin gwamnati da zaran sun kammala karatun su

- Ministan ilimi, Alhaji Adamu Adamu ya bayyana hakan a ranar Litinin, 5 ga watan Oktoba, 2020

- Haka zalika, shugaban kasar ya amince da bayar da gurbin karatu na kai tsaye tare da daukar nauyin karatun 'ya'yan malamai

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya amince a dauki daliban NCE aikin gwamnati kai tsaye da zaran sun kammala karatun su.

Ministan ilimi, Alhaji Adamu Adamu a ranar Litinin, 5 ga watan Oktoba ya bayyana hakan, a babban birnin tarayya Abuja, yayin bukin murnar zagayowar ranar malamai ta duniya.

KARANTA WANNAN: Jerin mutane 350 da suka mutu amma har yanzu ana biyansu albashi a Niger

Buhari ya amince a bawa daliban da suka yi karatun NCE aiki, ya kara shekarun aikin malamai
Buhari ya amince a bawa daliban da suka yi karatun NCE aiki, ya kara shekarun aikin malamai - @NGRPresident
Asali: Facebook

Haka zalika, shugaban kasar ya amince da bayar da gurbin karatu na kai tsaye tare da daukar nauyin karatun 'ya'yan malamai.

Shugaban kasar, ya kuma bayar da umurni da a kara kudin albashin malaman makarantar tare da tsawaita shekarun aikin su.

KARANTA WANNAN: Rundunar yan sanda ta samar da lambobin kira idan jami'anta sun ci zarafin ka

Legit.ng Hausa ta ruwaito maku cewa shugaban kasa Muhammadu Buhari ya amice da karin albashi ga malaman makaranta, ya sanar da hakan a murnar ranar malamai ta duniya.

Shugaban kasar ya kara wa'adin shekarun aikin malaman daga 35 zuwa 40, yayin da ya ke albishir da kara albashin malaman don basu kwarin guiwar gudanar da ayyukansu.

A wani labarin, Sashen kula da huldodin jama'a na rundunar 'yan sandan Nigeria ya samar da lambobin waya da kafofin dandalin sada zumunta da WhatsApp domin tabbatar da tsaftataccen aiki a rundunar.

Rahotanni sun bayyana cewa, rundunar ta samar da wadannan hanyoyin ne domin yin nazari da sa ido ga ayyukan sashen FSARS da sauran jami'an kwantar da tarzoma da ke cikin ta.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel