Fadar shugaban kasa ta yi martani mai zafi ga masu ikirarin Najeriya za ta tarwatse

Fadar shugaban kasa ta yi martani mai zafi ga masu ikirarin Najeriya za ta tarwatse

- Gwamnatin tarayya tayi ala-wadai da 'yan Najeriyan dake miyagun maganganu akan tarwatsewar kasa

- Mai magana da yawun shugaban kasa, Garba Shehu ya ce wadannan kalamai na nuna rashin kishin kasa

- Shehu yace a yanzu haka Shugaba Buhari ya tsaye tsayin-daka wurin ganin ya ceto Najeriya daga dukkanin baraka

Gwamnatin tarayya tayi ala-wadai akan 'yan Najeriyan dake cewa Najeriya na gab da tarwatsewa.

Garba Shehu, mai magana da yawun shugaban kasa ya fadi hakanne a wata takarda ta ranar Lahadi, 14 ga watan Oktoba wanda yake cewa rashin kishin kasa ne furta wadannan kalamai.

Gwamnatin tarayya ta zargi wasu 'yan Najeriya akan maganganun nuna rashin kishin kasa.

Garba Shehu ya ce gwamnatin Buhari ba za ta lamunci irin wadannan kalubalan ba.

Gwamnati zata tsaya tsayin-daka wurin kawar da duk wani abu da zai tada tarzoma da kuma hankulan 'yan kasa.

Ya ce gwamnati zata dage wurin kawar da matsalolin rashin tsaro da kuma cutar COVID-19.

Mai magana da yawun shugaban kasan, yace gwamnatin tarayya ba za ta dauki wani matakin da zai cutar da 'yan Najeriya miliyan 200 ba, wanda hakan ne abu na farko da Shugaban kasa ya dace yayi.

Shehu ya kara da cewa, "Buhari zai cigaba da dagewa wurin ganin ya kawo karshen duk wani kalubale dake damun Najeriya."

KU KARANTA: Ina alfahari da ayyukan cigaban da muka yi wa Najeriya tare da Obasanjo - Atiku

Fadar shugaban kasa ta yi martani mai zafi ga masu ikirarin Najeriya za ta tarwatse
Fadar shugaban kasa ta yi martani mai zafi ga masu ikirarin Najeriya za ta tarwatse. Hoto daga @GarbaShehu
Asali: Twitter

KU KARANTA: An kama dan sandan da je rubuta wa wani jarababawar UTME ta 2020

A wani labari na daban, wata kungiyar matasa 'yan jam'iyyar APC, sun zabi Bola Tinubu a matsayin shugaban da zai maye gurbin shugaban kasa Muhammadu Buhari a shekarar 2023.

Kungiyar matasan sun bayyana yadda yanzu haka suke fadi-tashin ganin sun ga lallai Tinubu ne zai tsaya a matsayin dan takarar shugabancin kasa a jam'iyyar APC a shekarar 2023.

Jaridar This Day ta bayyana yadda matasan suke kokarin ganin Tinubu ya maye gurbin shugaba Muhammadu Buhari idan wa'adin mulkinsa ya cika a shekarar 2023.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel