Yan sanda sun kama matar da ake zargi da yanka yaranta a Kano
- Rundunar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta tabbatar da kama matar da ake zargi da yi wa ‘ya’yanta biyu yankan rago
- Kakakin rundunar yan sandan jihar, DSP Abdullahi Haruna ne ya bayyana hakan a yau Lahadi
- Zuwa yanzu dai kwamishinan ‘yan sandan jihar, Habu Sani ya bukaci a mayar da binciken zuwa sashen binciken manyan laifuka
Rundunar yan sandan jihar Kano ta kama matar nan mai shekaru 26, Hauwa Habibu, wacce ake zargi da yi wa ‘ya’yanta biyu yankan rago a Kano.
Kakakin rundunar yan sandan jihar, DSP Abdullahi Haruna ne ya bayyana hakan a yau Lahadi, 4 ga watan Oktoba a garin Kano, jaridar Vanguard ta ruwaito.
Ya bayyana cewa a ranar 3 ga watan Oktoba, hukumar yan sanda ta samu labarin cewa wacce ake zargin ta sassara yaranta biyu har lahira da adda.
Haruna ya bayyana cewa yaran da abun ya cika da su sune Yusuf Ibrahim mai shekaru 6 da Zahra Ibrahim mai shekaru 3.
KU KARANTA KUMA: Girman kai rawanin tsiya: An hango gwamnan Kwara yana yankar ciyawa
“Da muka samu labarin, mun yi gaggawan tura jami’anmu zuwa wajen sannan suka gano cewa an caccaki yaran ne,” in ji shi.
Ya ce daga nan ne aka garzaya da su asibitin kwararru na Murtala Muhammad dake Kano inda likitoci suka tabbatar sun mutu.
Ya kuma ce matar ta yanki wata kanwarta mai suna Aisha Abdullahi mai shekaru 10 da adda wacce ita kuma aka kai ta Asibitin Koyarwa na Malam Aminu Kano dake Kano.
KU KARANTA KUMA: Zaben shugaban ƙasa 2023: Magoya bayan Buhari na son Jonathan ya dawo mulki
Hakazalika kakakin ya ce kwamishinan ‘yan sandan jihar, Habu Sani, ya bayar da umarnin a mayar da binciken zuwa sashen binciken manyan laifuka na rundunar domin fadada bincike.
A wani labari na daban, mun ji cewa wani abun tashin hankali ya afku a Unguwar Sheka da ke karamar hukumar Kumbotso na jihar Kano.
Mutanen wannan yanki dai sun tashi da alhini na mutuwar wani dan unguwar mai suna Sagir Muhammad wanda ake zargin wani matashi mai suna Abdullahi Muhammad da kashe shi.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng