Budurwa ta yi wa saurayi kaca-kaca a kan bata N15,000 na bikin murnar zagayowar ranar haihuwarta

Budurwa ta yi wa saurayi kaca-kaca a kan bata N15,000 na bikin murnar zagayowar ranar haihuwarta

- Wata budurwa ta yi wa saurayi wankin babban bargo sakamakon kyautar da ya bata na bikin zagayowar ranar haihuwarta

- Budurwa Tola ta caccaki saurayinta mai suna Babatunde bayan ya tura mata N15,000 a matsayin kyautarsa

- Ta bukaci kada ya sake kiranta har gaba da abada saboda ya kasance makwado wanda bai san darajar mace ba

Wata hira tsakanin budurwa da saurayi ta bazu a kafafen sada zumutar zamani wacce ta janyo tsokaci kala-kala daga jama'a, shafin Linda Ikeji ya wallafa hakan.

kamar yadda hirar ta nuna, budurwar ta yi wa saurayin wankin babban bargo a kan kyautar da ya bata domin bikin murnar zagayowar ranar haihuwarta.

Kamar yadda hirar ta nuna, budurwa Tola ta caccaki saurayinta mai suna Babatunde, bayan da ya yi mata murnar zagayowar ranar haihuwarta kuma ya tura mata N15,000.

Tola ta matukar tunzura a kan kyautar dubu goma sha biyar da ya bata kuma hakan yasa ta yi masa kaca-kaca tare da jan kunnensa da kada ya sake tuntubarta har abada.

Ta zargi Babatunde da zama namiji makwado kuma wanda bai san darajar mace ba.

Budurwa ta yi wa saurayi kaca-kaca a kan bata N15,000 na bikin murnar zagayowar ranar haihuwarta
Budurwa ta yi wa saurayi kaca-kaca a kan bata N15,000 na bikin murnar zagayowar ranar haihuwarta. Hoto daga @Lindaikeji
Source: Twitter

KU KARANTA: Gwamnoni sun kai wa Zulum ziyara, sun janjanta masa abinda ya faru da shi

Budurwa ta yi wa saurayi kaca-kaca a kan bata N15,000 na bikin murnar zagayowar ranar haihuwarta
Budurwa ta yi wa saurayi kaca-kaca a kan bata N15,000 na bikin murnar zagayowar ranar haihuwarta. Hoto daga @Lindaikeji
Source: Twitter

Budurwa ta yi wa saurayi kaca-kaca a kan bata N15,000 na bikin murnar zagayowar ranar haihuwarta
Budurwa ta yi wa saurayi kaca-kaca a kan bata N15,000 na bikin murnar zagayowar ranar haihuwarta. Hoto daga @Lindaikeji
Source: Twitter

KU KARANTA: Tsintar gawar mafarauci a daji ya tada hankulan mazauna Abia

Budurwa ta yi wa saurayi kaca-kaca a kan bata N15,000 na bikin murnar zagayowar ranar haihuwarta
Budurwa ta yi wa saurayi kaca-kaca a kan bata N15,000 na bikin murnar zagayowar ranar haihuwarta. Hoto daga @Lindaikeji
Source: Twitter

A wani labari na daban, wata budurwa 'yar Najeriya ta wallafa kyakyawan hotonta inda ta bayyana cewa tana nemawa kanta saurayi tare da kawarta.

A wallafarta a shafinta na Twitter mai suna @adannanwaokolo, ta lissafa irin namijin da take so kuma ya miko kokon bararsa.

Daya daga cikin yanayin mijin da take so shine ya kasance yana zama a tsibirin Legas, anguwar masu kudi ba ta talakawa ba.

"Barkanku, ni da kawata muna bukatar samari. Dole ne ya zama dogo, baki, mai aiki mai kyau, gwarzo a gado, yana zama a tsibirin Legas ba unguwar talakawa ba, mai gemu, mai kawatacciyar murmushi, mai shekaru daga 25 zuwa 30," ta wallafa.

Adanna ta bayyana cewa, dole ta sa ta fito ta yi wannan tallar saboda "A rashin tayi a kan bar arha."

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Online view pixel