Nigeria @ 60: FG ta bada umarnin toshe dukkan hanyoyin da za su kai Eagle Square

Nigeria @ 60: FG ta bada umarnin toshe dukkan hanyoyin da za su kai Eagle Square

- Gwamnatin tarayya ta dakatar da shige da ficen a dukkan wasu tituna da zasu kai ga Eagle square daga daren Laraba, 30 ga watan Satumba

- Ministan yada labarai da al'adu, Lai Muhammad ne ya bada wannan sanarwar saboda tabbatar da tsaro a wurin gagarumin cika Najeriya shekaru 60

- An bada wannan umarnin ne saboda shirye-shiryen shagalin bikin cikar Najeriya 60 da samun 'yancin kai ranar 1 ga watan Oktoba

Gwamnatin tarrayya ta bada umurnin dakatar da shige da fice a duk wasu hanyoyin da zasu kai Eagle square tun daga tsakar daren Laraba, 30 ga watan Satumba, don shiryawa bikin murnar cikar Najeriya shekaru 60 da samun 'yancin kai da za a yi a ranar Alhamis, 1 ga watan Oktoba.

Ministan yada labarai da al'adu, Lai Muhammad ne ya sanar da hakan domin tabbatar da tsaron ciki da wajen Eagle square, inda aka tsara yin shagalin bikin a cikin babban birnin tarayya, Abuja.

Sannan kuma, za'a dakatar da shiga titin Shehu Shagari, titin Ahmadu Bello, titunan shige da ficen tashoshin jiragen sama, duk wasu titunan dake haduwa da shiga babbar sakateriyar tarayya daidai karfe 2.00pm a ranar Laraba, 30 ga watan Satumba.

KU KARANTA: Durkusawar budurwa a gaban saurayi don karbar tayin aure ya janye cece-kuce

Nigeria @ 60: FG ta bada umarnin toshe dukkan hanyoyin da za su kai Eagle Square
Nigeria @ 60: FG ta bada umarnin toshe dukkan hanyoyin da za su kai Eagle Square. Hoto daga @Lindaikeji
Asali: Twitter

KU KARANTA: Rikicin APC a Ekiti: El-Rufai, Wase da Okorocha sun jagoranci kwamitin sulhu

A wani labari na daban, John Oyegun, tsohon shugaban jam'iyyar APC na kasa, ya ce mulkin shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kasance mara sa'a tun farkon shi.

A yayin zantawa da manema labarai a gidansa da ke Benin a ranar Litinin, ya ce ba don salon mulkin ba, da Najeriya bata samu cigaban da ta samu a yanzu ba, The cable ta wallafa.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel