Maimakon korafi: Ku taya ni yakar cin hanci da rashawa - Buhari ga 'yan Nigeria

Maimakon korafi: Ku taya ni yakar cin hanci da rashawa - Buhari ga 'yan Nigeria

- Shugaban kasa Buhari ya jaddada bukatar kawo karshen cin hanci da rashawa a Nigeria, yana mai cewa, cin hancin ya kawo koma baya a ci gaban kasar

- A cewar Buhari, akwai bukatar kowanne bangare na gwamnati, kai har ma da al'ummar kasar, su hada karfi da karfe, mai makon tsayawa yin korafi

- Buhari ya tariyo yadda ya kirkiri hukumar WAI a lokacin mulkin soja, wacce ya yi amfani da ita wajen kulle manyan jami'an kasar da suka sace kudin jama'a

Ma damar ana so Nigeria ta yi nasara a yaki da cin hanci da rashawa, to ya zama wajibi kowanne bangare ya bada hadin kai wajen cimma hakan, ko ba komai, Nigeria ce zuciyar Afrika.

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyana hakan a ranar Litinin, a lokacin da ya ke jaddada bukatar da ke da akwai, na kawo karshen cin hanci da rashawa a Nigeria.

A don haka, ya ce, akwai bukatar kowanne bangare na gwamnati, kai har ma da al'ummar kasar, su hada karfi da karfe, don kawar da cin hanci da ya addabi kasar.

KARANTA WANNAN: Matasa a yi hattara: Kotu ta garkame mashayin wiwi bayan kamashi da ita a Kano

Maimakon korafi: Ku taya ni yakar cin hanci da rashawa - Buhari ga 'yan Nigeria
Maimakon korafi: Ku taya ni yakar cin hanci da rashawa - Buhari ga 'yan Nigeria
Asali: Twitter

Shugaban kasa Buhari ya yi jawabin haka ne a Abuja a taron hukumar yaki da cin hanci da rashawa da dangoginsu, wato ICPC karo na biyu.

A yayin taron, an kuma kaddamar da kundin tsarin gudanar da rayuwa na kasa, musamman rayuwar da ta ci karo da laifukan cin hanci da rashawa, don magance matsalolin da suka shafa.

Hukumar ICPC ce ta tattara wannan kundi, tare da hadin guiwar ofishin sakataren gwamnatin tarayya (SGF) da kuma hukumar wayar da kan al'umma ta kasa (NOA).

KARANTA WANNAN: FG ta buɗe sabon shafin yanar gizo, ta ƙirƙiri manhajar wayar hannu - Pantami

Shugaban kasa ya kuma bukaci yan Nigeria da su hada hannu da gwamnati wajen dakile wannan annobar, mai makon tsayawa yin korafi, don kai kasar tudun mun tsira.

A cewar sa: "A lokacin da na ke mulkin soja, na yaki cin hanci da rashawa, kuma na kulle jami'an gwamnati da suka yi sama da fadi da dukiyoyin al'umma."

"Na gabatar da hukumar yaki da rashin da'a (WAI), wacce aka samar da ita don ladabtarwa da kuma tabbatar da da'ar al'umma da kuma tabbatar da yin aiki tukuru," cewar Buhari.

Shugaba Buhari, wanda ya nuna muhimmancin samar da hukumar ICPC, ya kuma nuna muhimmancin yin garambawul a fannin shari'a na kasar, don ya ki da rashawa.

A wani labarin, Tsohon gwamnan jihar Imo, kuma Sanata mai wakiltar Imo ta Yamma, Rochas Okorocha ya yi kira ga shugaban kasa Muhammadu Buhari da ya dauki kwakkwaran mataki kan hadimansa.

Rochas Okorocha, ya shawarci shugaban kasar, kan mukarrabansa da ba sa tsinana komai a bangarorin da aka nada su.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel