Zan bai wa 'yan Najeriya kariya ba tare da duba banbancin jam'iyya ba - Buhari

Zan bai wa 'yan Najeriya kariya ba tare da duba banbancin jam'iyya ba - Buhari

- Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya jaddada wa 'yan Najeriya cewa zai basu kariya ba tare da duba siyasa ba

- Ya sanar da hakan ne yayin da Gwamna Obaseki na jihar Edo ya kai masa ziyara a gidan gwamnati

- Ya ce ra'ayin 'yan Najerya ne kan gaba kafin komai, kuma kariyarsu ta rataya wuyansa ne

Shugaban kasa Muhammadu Buhari yace yana fatan babu wani dan Najeriya da zai wahala koda a wacce jam'iyya yake.

Shugaban kasar ya fadi hakan ne lokacin da Gwamnan jihar Edo, Godwin Obaseki ya raka mataimakinsa, Philip Shuaibu da wasu yan jam'iyyarsu don godiya ga shugaban kasar a Abuja.

Shugaba Buhari ya sha alwashin kokarta wa wurin ciyar da al'umma gaba a bisa gaskiya da amana.

Sannan ya roki jama'a dasu dage wurin bada hadin kai ga gwamnati don samun cigaban kasa.

Ya ce: "Nagode da ka kawo min mataimakinka da mabiyanka bayan buge jam'iyyata da kuka yi.

"Tabbas ya kamata in bi abinda yan Najeriya ke so, koda kuwa bana so. Saboda tabbatar da babu wani dan Najeriya da ya wahala.

"Daga rahoton da sifetan yan sanda ya bani, ya tabbatar min da anyi zaben gaskiya da gaskiya.

"Idan yan takara suna da kudin biyan mutane su zabesu, suje suyita yi. Kawai abinda banaso shine, a biya 'yan ta'adda kudi su je su tada hankulan jama'a.

"Ina so yan Najeriya su fahimci cewa, ina matukar girmama su a matsayinsu na yan kasar nan, kuma kamar yadda nayi rantsuwa, tsaronsu na hannun Ubangiji kuma yana hannun gwamnati, wadda na ke jagoranta."

Shugaban kasar ya lura, a matsayinsa na shugaba a jam'iyya mai ci, duk da sun rasa wasu jihohi, amma zai so ace ya bar suna mai kyau kuma yayi siyasa mai tsafta.

Zan bai wa 'yan Najeriya kariya ba tare da duba banbancin jam'iyya ba - Buhari
Zan bai wa 'yan Najeriya kariya ba tare da duba banbancin jam'iyya ba - Buhari. Hoto daga @Channelstv
Asali: Twitter

KU KARANTA: Hukumar jami'a ta dakatar da malami a kan zargin cin zarafi da dirka wa daliba ciki

A wani labari na daban, Shugaban kasa Muhammadu Buhari a ranar Juma'a, 25 ga watan Satumba, ya ce ya dauka alhakin lallasa APC da aka yi a zaben ranar Asabar da ta gabata na gwamnoni.

Shugaban kasar ya sanar da hakan a gidan gwamnati bayan karbar sabon gwamna jihar Edo, Godwin Obaseki, tare da mataimakinsa Philip Shaibu da wasu jiga-jigan jam'iyyar PDP.

Buhari ya ce a matsayinsa na babban jiigo a jam'iyyarsa, shine yakamata a dora wa laifin komai ballantan a lokacin da aka lallasa su a zabe.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel